1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kasar Haiti.

Zainab AM AbubakarMarch 3, 2004
https://p.dw.com/p/BvlY
Yantawayen Haiti na murnar mamaye biranen kasar.
Yantawayen Haiti na murnar mamaye biranen kasar.Hoto: AP

A yau an wayi gari da kasancewar yan tawayen na cigaba dayin sintiri a kann tutunan fadar kasar Haiti da port-au-Prince ,ayayinda shugabansu guy Philippe ya gabatar da kansa a matsayin sabon Hafsdan dakarun kasar,tare da barazanar kame Prime minsta.A sanarwar da yayi ta gidan Radion a daren Jiya,inda ya dinga yawo cikin mota mai budadden kai tsakanin unguwanni, Philippe yace haikokin kasar a halin yanzu haka suna hannusa.To sai dai mai Brian Concannon,wanda ya kasance mai gabatar da karar wani jamiin yan tawayen mai suna Louis –Jodel Cahamblain,a kisan kiyashi da akayi a shekarata 1994,ya bayyana cewa wannan itace bakar rana a idanun jamaar kasar ta Haiti,domin ana iya kashe dukkan wadanda sukayi fafutukan kafa democradiyya a wannan kasa.Chamblain yace yan tawayen zasu mamaye garin Soleil inda akasarin mutanen garin magoya bayan shugaba Aristide ne.

To sai dai Conel Dave Berger dake jagorantan sojin Amurka da suka fara sauka a Haitin bayan ficewan Shugaba Aristide zuwa Afrika ranar lahadi,ya bayyana cewa Amurkan na shrin kara yawan dakarunta a wannan kasa ,musamman bayan bayanan shugaban yan tawayen na jiya ta kafofin yada labaru.Wasu mazauna garin Cap Haitian dake hannun yan tawayen ta Arewaci,sun sanar da cewa jiragen Amurka masu kirar saukan ungulu na shawagi a sararin samaniyan yankin tun a jiya talata.Bugu da kari sojin na Amurka nacigaba da sintiri a wasu bangarorin tashan jirgin ruwa dake Port-au-Prince.

Dakarun Amurka dana Faransa dake jagoran dakarun kiyaye zaman lafiya da komitin Sulhu ta amince su kasance a wannan kasa,basu da umurni na kwance damarar yakin yan tawaye,sai dai su tabbatar da tsaro a manyan wuraretare da kare yan kasarsu dake kasar,tare da kayayyaki da kuma gine ginen gwamnati,acewar Col Berger da Commandan rundunar Faransa.amurka dai ta sanar da tura karin sojin ta 400,ayayinda Chile a nata bangare tace zata tura sojoji na musamman 120 zuwa Haiti a yau Laraba,Faransa tace sojojinta 420 da yansanda ne zasu kasance a haiti tsakanin yau zuwa karshen mako

To sai dai har ya zuwa wannan hali da ake ciki,tsohon shugaba Jean Aristide bai samu matsuguni ba a inda ake saran zai cigaba da zaman gudun hijira.yYanzu haka dai yana karbar mafakane a gidan gwamnatin janhuriyar Afrika ta tsakiya dake Bangui,inda nan ya yada zango bayan yin murabus daga Haiti dake cigaba da fuskantar rikicin siyasa.Ministan harkokin wajen Afrika ta tsakiya Charles Wenezoui ya bayyana cewa Aristide na cigaba da zama a gidan gwamnati,kana nan bada jimawa ba zaa samar masa talabijin da tauraron dan adam domin ya samu sukunin ganin halinda duniya take ciki.

Majiya daga Amurka na nuni dacewa Tsohon shugaban Haitin ya nemi mafaka a Moroko da Afrika ta gudu amma,dukkansu biyun sunki amincewa.Afrika ta kudu dai tace bata samu wata takarda na neman mafaka Aristide ba.