1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Kasar Somalia

December 13, 2006

Kungiyar Islama ta kasar Somalia ba baiwa gwamnatin Habasha waádin mako guda ta janye sojojin ta daga Somalia ko kuma su fuskanci yaki.

https://p.dw.com/p/Btx4
Mayakan Islama na kasar Somalia
Mayakan Islama na kasar SomaliaHoto: picture-alliance/dpa

Yan Islaman wadanda ke da karfi musamman a kudancin Somalia sun ce kasar Habasha ta jibge dakarun sojin a kalla 30,000 a kusa da garin Baidoa dake zama cibiyar gwamnatin rikon kwarya ta kasar. Kasar ta Habasha da kasashen turai da kuma majalisar dinkin duniya dukkanin su suna goyon bayan gwamnatin rikon kwaryar amma ikon ta bai wuce garin Baidoa ba.

Babban jamiín tsaro na kungiyar Islama Sheikh Yusuf Mohammad Siad ya shaidawa manema labarai a birnin Mogadishu cewa idan sojojin Habashan basu fice daga Somalia ba cikin kwanaki bakwai, labudda za su far musu da yaki har sai sun fatattake su daga kasar.

Fadar Addis Ababa ta gwamnatin Habasha ta baiyana matukar damuwa da wannan furuci, yayin da majalisar dinkin duniya ta yi kira ga yan kungiyar ta Islama da kada su fara yakin wanda jamaá da dama ke tsoron cewa yana iya bazuwa zuwa wasu sassa a yankin. Jakadan Majalisar dinkin duniya a Somalia Francois Lonseny Fall yace yana fata ba za su aiwatar da abin da zai kara dagula shaánin tsaro da dama ya riga ya tabarbare a kasar ta Somalia ba.

A watan Yunin da ya gabata ne yan Islaman suka kwace birnin Mogadishu gari mafi girma a kudancin Somalia wanda hakan ke yin barazana ga ikon gwamnatin rikon kwarya ta Shugaba Abdullahi Yusuf. Jakadu da kuma wadanda suka ganewa idanun su, sun ce dubban sojin kasar Habasha sun tsallaka kan iyaka domin bada kariya ga gwamnatin rikon kwarya ta Abdullahi Yusuf a ciki da wajen garin Baidoa. To amma Gwamnatin a birnin Addis Ababa ta ce sun tura yan daruruwan jamian soji ne kawai domin bada shawara.

P/M Habasha Meles Zenawi ya yi fatali da waádin kwanaki bakwai da yan Islaman suka baiwa gwamnatin sa ta janye sojojin ta ko kuma su gamu a filin daga. Yana mai cewa ko kadan wannan ba zai razana shi ba. Yace ai dama can yan Islaman sun sha yin irin wannan barazana, kuma ba yau suka fara kaiwa sojin Habasha hari ba. Yace su dai manufar su ita ce samun warware matsalar cikin ruwan sanyi, amma zai kasance babban abin bakin ciki idan baá iya sasanta rikicin kasar ta Somalia ba.

Yayin da ake cigaba da sa toka sa katsi da kuma fargabar barkewar yaki tsakanin yan kungiyar Islama na kasar Somalia da kuma kasar Habasha, tawagar kungfiyar tarayyar Turai wadda ta kai ziyara Mogadishu babban birnin Somalia ta yi kira ga kungiyar ta Islama wadda ke kara samun karfi ta koma shawarwarin sulhu da gwamnati domin dorewar zaman lafiya a kasar. Jamiín harkokin waje na kungiyar Islaman Ibrahim Hassan Adow yace yace zaá cigaba da fuskantar mummunan tashin hankali matukar Habasha bata janye sojojin ta daga Somalia ba.