1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kasar Sri Lanka

October 18, 2006
https://p.dw.com/p/BufT
Rundunar sojin saman kasar Sri Lanka ta kai karin farmaki akan wuraren da ake zargin cewa na ´yan tawaye ne dake gabashin kasar. Majiyoyin ´yan tawaye sun ce an kashe mutum guda yayi da aka jiwa biyu rauni ciki har da yaro karami. Rundunar sojin Sri Lanka ta musanta cewa ta kai hari akan wuraren farar hula. Farmakin ta sama ya zo ne sa´o´i kadan bayan da wasu da ake zargi ´yan tawayen Tamil Tigers ne a cikin kwale-kwale sun kutsa cikin wata tashar jirgin ruwa kuma sun kai hari kan wani sansanin sojin ruwan kasar dake garin Galle wata cibiyar ´yan yawon shakatawa dake kudancin kasar. Yanzu haka dai hukumomi sun kafa dokar hana fita a garin na Galle don hana ta da wata tarzoma. Farmakin dai ya zo ne gabanin taron tattauna shirin zaman lafiya da za´a yi a karshen wannan wata a birnin Geneva tsakanin gwamnatin Sri Lanka da ´yan tawaye.