1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin koma bayan arzikin Girka

March 17, 2010

Tsuke bakin aljihun gwamantin Girka na ci gaba da haifar da zanga-zangar ma´aikatan ƙasar

https://p.dw.com/p/MUnE
Tsaba ta kuɗin EuroHoto: DW

Al´umar ƙasar Girka na ci gaba da zanga-zanga don nuna ɓacin ransu game da matakin tsuke bakin aljihu da gwamanti ta ɗauka. Aƙalla mutane 2000 ne suka yi takun saka da jami´an tsaro a gaban majalisan dokoki da ke birnin Athenes domin yin Allah wadai da ragin albashi da kuma soke panshon waɗanda suka yi ritaya. Jami´an tsaro sun yi amfani da borkonon tsofuwa wajen tarwatsa gungun matasa da ke harbe harbe da duwatsu. Wannan tayar da ƙayar bayan ya zo ne a daidai lokacin da ministocin kuɗi na ƙasashen da ke da kujera a ƙungiyar gamayyar Turai suka kammala wani taronsu na yini biyu a Brussels a inda suka tsayar da shawara game da tallafin kuɗi da za su bai ma mambobin EU idan suka sami kansu cikin wadin tattalin arziki.

Ministocin suka ce sun yi imanin cewa ƙasar Girka za ta yi nasarar tsame kanta daga wannan koma bayan tattalin arziki da ta sami kanta a ciki. Ministan kuɗi na ƙasar Girka ya baiyana cewa tattalin arziƙin ƙasarsa ya fara murmurewa tun bayan ɗaukan matakan na tsuke bakin aljuhu. Girka dai ita ce ƙasar Turai ɗaya tilo da ke amfani da takardar kudin Euro da rugujewar bankuna ya kawo rauni ga tattalin arziƙinta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Yahouza Sadissou