1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Koriya ta Kudu da kuma Koriya ta Arewa

November 29, 2010

Shugaban Koriya ta Kudu ya ce zai sa ƙafar wando guda da Koriya ta Arewa idan ta sake takalar ƙasarsa da faɗa.

https://p.dw.com/p/QKfT
Shugaba Lee Myung-bak na Koriya ta KuduHoto: AP

Shugaba Lee Myung -bak na Koriya ta Kudu ya yi alƙawarin ladabtar da Koriya ta Arewa matiƙar ta sake kai ma wani ɓangare na ƙasarsa hari makamancin na makon da ya gabata. Cikin wani jawabi da ya yi wa al'umar ƙasarsa ta kafafen watsa labarai a karon farko tun bayan fara rikicin, Shugaba Lee ya ce ƙasarsa ba za ta ƙara ƙyale wata ƙasa maƙwabciya ta ci mata kashi a tsakar ka ba.

Masu lura da harkokin diflomasiya sun danganta kalaman na shugaban Koriya ta Kudu da hannunka mai sanda ga ƙasar China da ke neman a sulhunta rikicin cikin ruwan sanyi. Ana ganin cewa shugaban na Koriya ta Kudu ya yi fatali da tayin da China ta yi masa na gudanar da taron gaggawa tsakanin ƙasashe shidda domin warware taƙaddamar makaman Nukliya na Koriya ta Arewa. Ita dai ƙasar ta China ta nemi ɓangarorin biyu da kuma masu shiga tsakanin sun zauna kan teburi guda domin samar da maslaha ta hanyar diflomasiya akan kai ruwa rana da ake yi tsakanin Koriya ta Kudu da ta Arewan.

Wanan matakin ya biyo bayan hauhawar ƙamarin dangantaka tsakanin Koriyoyin biyu-sakamakon hallaka mutane huɗu da Koriya ta Arewa ta yi a lokacin da ta yi ruwan rokoki a wani tsibiri na Koriya ta Kudu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Halima Balaraba Abbas