1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Kwango ya jefa 'yan kasar cikin yunwa

Abdul-raheem Hassan
July 19, 2017

'Yan kasar Jamhuriyar Demokradiyar Kwango na fama da karancin abinci, inda a yanzu rikicin kabilanci ya tilasta wa dubban 'yan kasar tsallakawa izuwa kasashe makota dan yin gudun hijira.

https://p.dw.com/p/2gpOk
UNHCR Südsudan Flüchtlinge
Hoto: Getty Images/AFP/I. Kasamani

A yanzu dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewar sama da mutane dubu 150,000 ne ke bukatar agajin gaggawa, yayin da akalla sama da 'yan kasar dubu 50 suka tsere wa matsugunan su. A jiya ne dai gwamnatin kasar Kwango tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya, suka kaddamar da asusun tallafin gaggawa da ke bukatar kudi dalar Amirka miliyan 23.

A cewar hukumomin dai kudaden za su taimaka a ceto rayuwar dubban fararen hula a yankunan da rikicin ya fi kamari, to sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta nuna kaduwar ta kan yadda rahotannin kungiyoyin fararen hula ke ambato sojojin gwamnati wajen cin zarafin al'umma da keta haddin mata, amma kawo yanzu gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyar Kwango ba ta ce komai a kan wannan zargi ba.