1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kwango ya ritsa da sojan Ghana ɗaya

April 4, 2010

Wani sojan Ghana ya gamu da ajalisan a arangama tsakanin jami´an tsaro da yan bindiga a arewa maso gabashin Kwango.

https://p.dw.com/p/Mn9U
Kiyaye zaman lafiya a KwangoHoto: AP

Wani sojan Ghana da ke aikin kiyaye zaman lafiya a Jamhuriyar Demokaraɗiyar Kwango ya rigamu gidan gaskiya, a lokacin taho mu gama tsakanin dakarun gwamanti da kuma mayaƙan sa kai. Dakarun na Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kwango sunyi musayar wutan ne da mayakan ƙabilanci kimanin 100, a garin Mbandaka da ke arewa maso gabashin ƙasar , yankin da aka fuskanci rikicin ƙabilanci a bara. Rikicin dai ya ɓarke ne bayan da jami'an tsaro suka gano kwale-kwalen dake ɗauke da 'yan adawan da aka yi jigilarsu daga birnin Kinshasa i zuwa wannan yanki.

Ministan cikin gida wato Guy Inenge, ya nunar da cewa ya zuwa yanzu yan bindiga daɗin, sun tsere zuwa cikin ƙauyuka dake yankin. A watan Oktoba ne dai rikici ya ɓarke tsakanin ƙabilun Lobala da kuma Monzaya, tare da haddasa mutuwan mutane 270, a yayinda aka tilastawa wasu dubu 187, barin matsugunnensu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala