1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Makamashin Nukiliyar Iran

February 9, 2010

Ƙasashen Duniya sun yi barazanar kakabawa Iran takunkumi na tattalin arziki

https://p.dw.com/p/Lx0a
Mahmoud Ahmadinejad )Hoto: AP

A yau ne Iran ta ƙaddamar da gine-ginen sabbin tashoshin sarrafa makamashi har guda goma a faɗin ƙasar a wani yunƙuri na fara bunƙasa kashi 20 daga cikin 100 na Uranium da ta mallaka. Sai dai ƙasashen yammacin Duniya sun nanata cewa Iran bata da hurumi, a saboda suka ce za su nemi Majalisar Ɗunkin Duniya ta ƙaƙaba mata takunkumin tattalin arziƙi.

A tashar sarrafa makamashi na Natanz da ke tsakiyar ƙasar ta Iran ne hukumomin taheran suka aiwatar da yunƙurinsu na mallakar makashin da suka ce zai taimaka wajen kyautata makomar yan ƙasar ta fannonin lafiya da kuma wadatan wutan lantarki. Alhali kuwa har i zuwa ƙarshen makon da ya gabata, ƙasashen yammacin Duniya sun kyautata zaton cewa Iran za ta bayar da kai ga bukatarsu na miƙa Uranium din ga ƙasashen Rasha da kuma Faransa domin su inganta mata shi. Amma kuma sai Iran ta sa ƙafa ta yi fatali da shi, ta na mai danganta shi da wani yunƙuri na tauye mata hakki. A saboda haka ne bisa sa idon jami´an IAEA, suka ƙaddamar da aikin na inganta makamashin. Haka zalika kuma sun sha alwashin kammala gina sabbin tasoshin sarrafa makashi kan nan da shekara mai zuwa. Shugaban hukumar makamshi ta Iran, wato Ali Akbar ne ya ɗauki nauyin sanar da lokacin da inda Ahmedinejad da maƙarrabansu suka sa a gaba.

IAEA stimmt gegen Irans Nuklearprogramm
Ali AsgharHoto: AP

"Ya ce muna bayyana ma duniya cewa mun aiki da sako a rubuce zuwa ga hukuma mai lura da hana yaɗuwar makaman nukuliya cewa mun ƙudiri aniyar bunƙasa kashi 20 daga cikin 100 na uranium da muka mallaka. Tare da sa idon jamai´an IAEA, za mu fara inganata sanadarin a aranar talata idan Allah ya yarda."

A halin da ake ciki dai, ƙasashen yammacin duniya suna gudanar da shawarwari tsakaninsu domin ganin yaddda za su ɓullo ma lamarin ɓunƙasa Urinium na Iran da wasunsu ke dangantawa da ƙoƙarin neman mallakar makamshin nukuliya. Tuni dai ƙasashen Faransa da kuma Amirka suka bayyana aniyarsu na neman MDD ta ƙaƙaba wa Iran wani sabon takunkumin karya tattalin arziƙi. Sai dai China da ke da ikon hawa kan kujeran na ƙi ta ce hanyar diplomasiya ita ce mafi a´ala na warware wannan taƙaddamar sanadarin Uranium na Iran. Ita ma Jamus ta baiyana matakin da cewa alama ce dake nuna cewa Iran bata da niyyar bada haɗin kai ga gamaiyar ƙasa da ƙasa a saboda haka tace akwai buƙatar sanya mata sabbin takunkumi. Sai dai Asghar Soltani wani ficecen ɗan siyasan Iran, ya ci kin mutanta sharuɗan da Teheran ta ƙaƙaba musu da ƙasshen yamma ba su yi bane, ya sa su canza shawara.

IAEA stimmt gegen Irans Nuklearprogramm
Mohamed ElBaradei da Guido WesterwelleHoto: AP

" za muna da ƙarfin samar da makamashin ta hanyar bunƙasa kashi 20 daga cikin 100 na sanadrin na Urinium tun watanni taran da suka gabata. Amma ba mu yi ba, domin mu shafe wannan lokaci muna bayar da damar samun bakin zaren warware rikicin ƙarƙashin hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai lura da hana yaɗuwar makaman Nukiliya. Tun da ba a biya mana bukatunma, mu kuma mun zaɓi yin gaban kanmu."

Shi dai shugaban IAEA ya nuna damursa game da ƙudirin Iran na fara bunƙasa kashi 20 cikin ɗari na sinadarin Uranium da ta mallaka. Yukiya Amano ya ce ko shakka babu wannan yunƙuri na Teheran zai yi karar tsaye ga burin da aka sa a gaba na neman taƙaita makaman nukiya a duniya. watanni tara aka shafe ana kai kawo tsakanin Iran da ƙasashen yamma ba tare da cimma biyan bukata ba.

Mawallafi: Mouhammadou Awal Balarabe

Edita: Zainab Mohammed