1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin matasan musulmi a Islamabad

July 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuH3

Jamian tsaro a Pakistan sun yi kira ga matasa yan takife waɗanda suka yi mafaka a masallacin Lal Masjid a birnin Islamabad da su miƙa kan su cikin girma da arziki. A ƙalla mutane 16 suka rasa rayukan su a musayar wuta tun bayan ɓarkewar rikicin a ranar talatar da ta wuce. Jamián tsaron Pakistan sun kuma sanar da cewa sun kama limamin masallacin Abdulaziz a lokacin da yake ƙoƙarin tserewa. Tuni dai wasu dalibai kusan dubu daya a harabar masallacin suka miƙa kan su ga hukuma, bayan da suka amince da tayin da aka yi musn na ficewa salin alin tare kuma da basu kuɗi rupees 5,000 Jagoran masallacin mai matsanancin raáyi na neman ɗabbaƙa tsarin shariár musulunci irin na Taliban a Islamabad babban birnin ƙasar ta Pakistan.