1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin mayakan Sa kai da Dakarun gwamnati a Basra

Shuaibu Othman SamboMarch 26, 2008

Sama da mutane 40 ne suka rasa rayukansu a arangama tsakanin dakarun gwamnatin Iraki da mayakan ɗarikar Shi'a

https://p.dw.com/p/DVAI
Yakar sojin sakai a BasraHoto: AP


Tun bayan da gwamnatin Iraƙi ta buƙaci masu ɗauke da makamai a kasar da su mikasu ga hukuma tare da umartar jami'ain tsaro da su kewaya domin karbar makamain a farkon makon nan ,sabon rikici ya barke a garin Basra da kewaye a sakamakon binciken da jami'ain tsaron kasar Iraki ke gudanarwa don karbe makamai daga hannun fararen hula.

Rikici tsakanin jami'ain tsaron gwanatin Iraqi da mayakan sakai na kungiyar Darikar shi'a ta mahdi da ke karkashin jagorancin Muktada Al-sadr ya cigaba da karuwa har zuwa larabar nan tun daga jiya ,biyo bayan umarnin Firayin Minista kasar Nuru Al maliki ga jamiain yan sanda da su kewaya yankunan daban daban na kasar domin karbe makamai daga hannu fararen hula a kokarin gwamnatin na kawo karshen yawan kashe kashen da ake samu yayin fadace fadace a tsakanin bangarorin da ke adawa da juna.

Wannan rikici yanzu haka yacigaba dabazuwa zuwa wasu sassan da ke makwabtaka da garin Basra musamman yankunan da magoya bayan muktada sadr suke da rinjaye kamar kut,garin da bai wuce tazaran kilomita 175 daga Bagadaza Babban birnin Iraki.ko da yake kusan za iya cewa gwamnati Iraki ta kaddamar da wanna shirin karbe makamai ne musamman domin magaya bayan kungiyar ta mahdi kasancewar su wadanda suka fi tada kayan baya da kuma anfani da makamai a tsakanin mabiya addinan kasar.


Yau an wayi gari komai ya tsaya cik a garin Basra makarantu a rufe ,kasuwanni da shaguna duk a rurrufe duk kuwa da cewar dokar hana yawon dare da gwamnati ta sana yana karewa ne da karfe shida na safiya.


A wata sabuwa,shiek muktada Sadr ya yi kira da koma teburin tattaunawa domin kawo karshen wannan rikici na Basra,inda ya bukaci cewa PM NuruMaliki da ya fice daga birnin inda yake sanya idanu da kansa kanyadda aikin amshe makaman daga hannu yan shia ke gudana. daidai lokacin da magoya bayansa ke cigaba da artabu da dakarun gwamnati a garin Basra mai tashar jiragen ruwa a kudancin irakin.

Anji daga bakin kakakin gwamnati Iraki Ali Dabbagh yana mai fadin cewar :

"PM da kansa ne ya ke jan akalar matakin kuma ba zai bar garin ba Basran ba sai idan kura ta lafa.kazalika matakin zai kawo karshen sa ne bayn an samu sararawar al'amura"

Rahotannin baya bayannan na nuni da cewar mayakan kungiyar mahdin sun fadada hare-haren da suke kai wa kan jami'ain tsaron zuwa Bagadaza inda suka harba Rokoki cikin babban birnin dab da fadar Gwamnati lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar kimanin mutane takwas wasu Ashirin da biyar kuma suka jikkata.,wadanda suka hada da wasu yan kasar Amurka uku.

Ita kuma gwamnatin Iraki ta baiwa mayakan shia wa'adin sa'o'i 72(kwanaki uku) da su mika makamansu ko kuma doka ta yi aiki kan duk wanda aka kama yaki bin wannan umarni.

Wannan rikcin ko kuma bijirewa da yan mahdin suke yi ya sanya babbar alamar tambaya a kan alkawarin daina kai hare-hare da Muktada Sadr ya bayyana a watan Agustan shekarar da ta gabata wadda kuma ya kara jaddada wa a watan jiya.