1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Niger Delta

January 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuUF

Rahoto daga yankin Niger Delta a taraya Nigeria, sun ce wani ɗan ƙasar Nederland, ya rasa ran sa, tare da yan Nigeria 3, a hare haren da matasan ƙungiyar MEND su ka kai, tsakanin Patakul da Bonni.

Yankin Bonni da ke kudancin Niger Delta, na ɗaya daga yankunan da ke da mahimamnci, wajen lodin ɗanyan man da Nigeria ke hiddawa, zuwa ƙasashen ƙetare.

Idan dai ba a manta, yankin Niger Delta, na fuskantar tashe tashen hankulla, a sakamakon ƙaya bayar, da matasa masu fafatakar ƙwato yancin yankin su ka tada.

A shekara da ta gabata, a ƙala sojojin Nigeria 37 su ka rasa rayuka, cikin arangama tare da ƙungiyoyin matasan yankin.

A yanzu haka, ƙungiyar MEND, na ci gaba da garkuwa da wasu ma´aikatan ƙasashen ƙetare, da su ka haɗa da 3 yan ƙasar Italia, 1 na Libanon da kuma 5 yan ƙasar Sin.

A wani labarin kuma,kotun a birnin Taraya Abuja ta gurfanar da Mohamed damagun shugaban jaridar Daily Trust, da ta ke zargi da ta´adanci.