1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin nukiliyar Iran

February 2, 2006

A yau hukumar IAEA ta fara bitar rikicin nukiliyar Iran

https://p.dw.com/p/Bu1s
Hukumar IAEA ta fara taronta akan Iran
Hukumar IAEA ta fara taronta akan IranHoto: AP

Kwamitin sulhu na MDD dai shi ne aka dora masa alhakin dinke barakar da kan samu a dangantaka ta kasa da kasa, kuma kasashen Amurka da Rasha da Birtaniya da Faransa da kuma China dake da dawamammen wakilci a kwamitin hade da sauran kasashe goma da ba na dindindin ba sune wadanda ainifin wadanda alhakin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya ya rataya a wuyansu, kamar yadda kudurin majalisar ya tanada.

Kwamitin na da matakai iri dabam-dabam wajen tinkarar matsalolin da ka iya zama barazana ga makomar lafiyar duniya. A baya ga matakai na diplomasiyya da na soja, kazalika kwamitin kan dauki matakai na takunkumi, da suka hada da tsinke dangantakar diplomasiyya ko karya tattalin arzikin kasa kamar yadda ya faru dangane da kasar Iraki a shekarun 1990. To sai dai kuma ire-iren wadannan kudurori na kwamitin sulhu na tattare da hadari. Misali dakatar da cinikin mai da kasar Iran ba kawai zai tabarbara kasafin kudin kasar ne ba, kazalika su ma kasashe masu ci gaban masana’antu da sauran masu amfani da motoci a sassa daban-daban na duniya zasu sha fama da radadin lamarin. Domin kuwa kasar ta Iran ita ce ta hudu a tsakanin jerin kasashen da suka fi cinikin mai a duniya. Akalla wajibi ne wakilai tara na kwamitin sulhu su ba da goyan baya kafin a aiwatar da wani mataki na takunkumi sai dai idan daya daga cikin dawwwamammun wakilansa ya haye kujerar na ki. A baya-bayan nan dai kasashen Rasha da China dake da ikon hawa kujerar na ki sun bayyanar a fili irin muhimmancin dake akwai game da dangantakarsu ta tattalin arziki da kasar Iran.

Amma kafin a kai sabanin da ake da kasar Iran akan shirinta na makamashin nukiliya gaban kwamitin na sulhu tilas ne a saurari rahoton hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa a farkon watan maris mai zuwa. A shekarar da ta gabata an ba wa hukumar lambar yabo ta Nobel don fafutukar neman zaman lafiyar duniya. Hukumar na ba da goyan baya ne ga hadin kan kasashe wajen aiwatar da tashoshin makamashin nukiliya ta hanyoyin lumana. Kasar Iran na da hannu akan wannan yarjejeniya kuma ta haka ya wajaba akanta tayi amfani na tashoshin nata na nukiliya domin samar da makamashi kawai. A dai halin da ake ciki yanzun da wuya hukumar makamashin nukiliyar ta kasa da kasa ta iya ba da wata shaidar dake tabbatar da cewar Iran na neman kauce wa wannan manufa. Domin kuwa har yau kasar bata albarkaci yarjejeniyar hana yaduwar fasahar sarrafa makaman nukiliyar da ta rattaba hannu kanta misalin shekaru biyu da suka wuce ba, wadda ita ce zata ba wa jami’an hukumar kai ziyarar ba zata a tashoshin makamashin nukiliyar wannan kasa.