1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin nukiliyar kasar Iran

January 8, 2006
https://p.dw.com/p/BvDG
Iran ta ce ta na da niyar bude wasu tashoshinta na nukiliya a daidai lokacin da ta sha alwashin sake fara aikin binciken karafan nukiliya. Wannan dai zai zama karo na biyu a cikin watanni kalilan da Iran ta bijirewa toshe tashoshinta na nukiliya da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta yi. Kasashen Turai karkashin jagorancin Jamus da Birtaniya da kuma Faransa sun gargadi Iran da ka da ta kuskura ta fara aikin sarrafa sinadarin uranium, to amma gwamnati a birnin Teheran ta dage cewar tana bukatar makamashin nukiliyar don samar da wutar lantarki. Amirka na zargin Iran da shirin kera makaman nukiliya a asirce.