1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Nuklear Iran

March 9, 2007
https://p.dw.com/p/BuQ8

Ƙasashe 5 masu kujerun dindindin a komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, tare da Jamus sun kasa cimma daidaito, a kann hanyoyin warware rikicin makaman nuklear ƙasar Iran.

Tun ranar litinin da ta wuce, jikadodin ƙasashen su ka fara saban taro, a birnin New-York na Amurika,wanda ya watse a yammacin jiya, baran-baram, ba tare da cimma masalaha ba.

Saidai jikadan ƙasar Rasha a Majalisar Ɗinkin Dunia, ya nunar da cewa duk, da saɓanin ra´ayoyin da a ke fuskanta, akwai ci gaba mai inganci da a ka samu.

Sabin matakan da ƙasashe ke bukatar ɗauka a kan Iran sun haɗa da saka takunkumin yin bulaguro ga wasu jami´o´in ƙasar ta Iran , da na hana shigi da ficin makamai, da kuma karya tattalin arziki.

Ƙasashen Sin da Russie, wanda ke goyan bayan Iran, sun nuna rashin amincewa da wasu daga cikin wannan matakai.

Jikadan Ƙasar Sin, ya bayana cewar ƙasashen 6 za su komawa kan tebrin shawarwari tun gobe juma´a, domin ci gaba da mahaurori akan wannan rikici.