1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin sakakon zabe a Liberia

Zainab A MohammadNovember 14, 2005

Masaniya kan tattalin arziki kuma tsohuwar ministan kudi ,itace ta lashe zaben shugaban kasa a Liberia

https://p.dw.com/p/Bu4B
Hoto: AP

Shugabannin kasashen Afrika sunyi kira ga alummar Liberia dasu gudanar da harkokinsu cikin lumana ,tare da watsi da tayar da hankula ,adangane da sakamakon zabe zagaye na biyu a wannan kasa.

Wannan kira da shugabannin kasashen Afrikan sukayi dai bazai kasa nasaba da korafe korafe da dan takara George Weah da magoya bayansa keyi na cewa an tabka magudi dangane da bawa fitacciyar masaniya kan tattalin arzikin kasar Ellen Johnson Sirleaf nasara ba.

Duk dacewa a hukumance baa sanar da sakamakon zaben na Liberia ba,bisa dukkan Alamu tsohuwar minister kudi mai kimanin shekaru 67 da haihuwa ,itace zata kasance mace ta farko akan mukamin shugabancin kasa a nahiyar afrika,a dangane da mafi yawan kuriu da hukumar zaben kasar tace ta samu ,fiye da abokin takaranta ,kuma sanannen dan kwallo George Weah.

To sai dai tsohon dan kwallon mai shekaru 39 da haihuwa,wadanda magoya bayansa sukayi ta jifan yansanda da duwatsu a birnin Monrovia a ranar jumaa,ya gudanar da wata yar zanga zanga aranar asabar,inda ya bukaci a sake gudanar da zaben baki daya,domin an tabka magudi.

Amma shugabannin Afrika a wani taron da suka gudanar a karshen mako a birnin Abujan Nigeria,sun yabawa yadda zaben na ranar talata ya gudana,abunda suka kira zaben shugaban Liberia cikin gaskiya da adalci.,wanda ke zama na farkon irinsa tun bayan kawo karshen yakin basasan wannan kasa dake yammacin Afrika.

Sanarwar shugabannin afrikan na kira gay an Liberia dasu darajawa wannan kokari da sukayi ,ta hanyar cigaba da gudanar da harkokinsu cikin lumana.

Shugabannin da suka gudanar da wannan taro daya kare a daren jiya lahadi a Nigeria dai sun hadar da Olusegun Obasanjo,da Thabo Mbeki na Afrika ta kudu da Abdoullaye Wade na Senegal da John Kufor na gana da wasu shugabannin kasashen Afrika.

Tun da farko a birnin Monrovian dai Pastocin darikun katholika da protestant ,sunyi gira ga magoya bayan addinan nasu dasu guji wani riki na siyasa daka iya tada zaune tsaye,wanda zai iya zubar da jinni kamar yadda aka fuskanta a lokacin yakin basasar kasar,wanda kuma aka kawo karshensa shekaru biyu da suka gabata.

A dangane da hakane Bishop Issac Winker ya fadawa magoya bayan darikarsa cewa ,akwai bukatar zaman lafiya a daidai wannan lokaci na jaririyar democradiyya da ake shirin kafawa a Liberia.

Tuni dai jammiyar George Weah ta CDC ta gabatar da kokenta a hukumance,gaban hukumar zabe mai zaman kanta na Liberian.

To sai dai tun da yammacin jiya ne manyan motoci kirar akori kura dauke da nauran Magana cike da magoya bayansa,ke yawo cikin birnin Monrovia ,domin kira ga magoya bayan jammiyar dasu halarci gangamin da suka shirya gudanarwa yau domin bayyana adawansu dangane da sakamakon wannan zabe daya ba Ellen Johnson Sirleaf nasara.

Akan hakane shugabannin kasashen Afrika a yayin taron nasu na Abuja wanda ya hadar da shugaban kungiyar gamayyar Afrika Alpha Umar Konare suka jaddadawa yan kasar Liberian muhimmancin amfani da kundun tsarin mulkin kasar da tsarin sharia wajen gabatar da korafinsu dangane da sakamakon zaben.