1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin shirin nukiliyar Iran

May 4, 2006
https://p.dw.com/p/Buzh
Kasashen Faransa da Birtaniya da kuma Amirka sun gabatarwa kwamitin sulhun MDD sabon daftarin kuduri game da shirin nukiliyar Iran. Har in dukkan membobin dake da kujerun dindindin a MDD suka amince da wannan daftarin to yana iya zama wani kuduri karkashin sashe na 7 na dokokin Majalisar ta Dinkin Duniya. A cikin kwanakin nan Amirka na ta kara matsa kaimi don ganin an zartas da wani kuduri wanda zai ba da damar sanyawa Iran takunkumi idan taki dakatar da shirin ta na inganta sinadarin uranium.