1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin shirin nukiliyar Iran

April 29, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0E

Kwana daya bayan cikar wa´adin da kwamitin sulhu ya bawa Iran, shugaba Mahmud Ahmedi-Nijad ya sake jaddada matsayin kasar sa game da shirinta na nukiliya. A lokacin da yake magana a birnin Teheran Shugaba Ahmedi-Nijad ya ce Iran zata kare ´yancin ta na mallakar fasahar nukiliya don amfanin fararen hula. Da farko mataimakin shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran Mohammed Saidi ya ce nan da makonni 3 masu zuwa gwamnati a birnin Teheran zata gabatarwa hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wani shiri da nufin warware takadamar da ake yi dangane da shirin ta na nukiliya. To amma bisa sharadin cewa kwamitin sulhun MDD bai sake yin wani zama akan wannan batu ba. A jiya juma´a wa´adin da aka ba Iran na dakatar da shirin tace sinadarin nukiliya ya kare. A ranar 9 ga watan mayu kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu zasu yi taro inda zasu tattauna akan mataki na bai daya da za´a dauka kan Iran din.