1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin shirin nukiliyar Iran

April 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1v

Shugaban Iran Mahmud Ahmedi Nijad ya sake nuna adawa da wanzuwar kasar Isra´ila tare da nuna shakku game da aukuwar kisan kiyashin da aka yiwa yahudawa. A lokacin da yake jawabi a gun wani babban taron tallafawa Falasdinawa a birnin Teheran shugaba Ahmedi-Nijad ya ce kasar Bani Yahudu na kan hanyar tarwatsewa. A dangane da takaddamar da ake yi akan shirin nukiliyar Iran kuwa sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta yi kira ga kwamitin sulhun MDD da ya zartas da wani kuduri wanda zai ba da damar yin amfani da karfin soji akan gwamnatin Teheran. A kuma halin da ake ciki Rasha ta gayyaci Amirka da KTT da kuma China zuwa wata sabuwar tattaunawa akan shirin nukiliyar Iran din da ake kace nace a akai. A ranar talata mai zuwa ake sa ran gudanar da wannan taro a birnin Mosko da nufin kauracewa aukuwar wani rikici.