1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin shirin nukiliyar Iran

January 27, 2006
https://p.dw.com/p/BvAg
China ta ce tana adawa da ra´ayin Amirka na kakabawa Iran takunkumi a dangane da shirin ta na nukiliya. Kakakin ma´aikatar harkokin wajen China Kong Quan ya fadawa manema labarai a birnin Beijing cewa China na goyon bayan wani shirin Rasha na sarrafawa Iran sinadarin uranium a Rasha a matsayin wata hanyar warware takaddamar da ake yi akan shirin nukiliyar na Iran. China ta bayyana haka ne yayin wata ziyara da mai shiga tsakani a shawarwarin nukiliya na Iran Ali Larijani ya kai birnin Beijing. Da farko jakadan Amirka a MDD John Bolton ya ce zai nemi goyon bayan sauran kasashe da su amince a yi karar Iran a gaban kwamitin sulhun MDD ko da Iran din ta amince da shirin na Rasha. A matsayin ta na mai kujrar dindindin a kwamitin Sulhu, China ka iya hawa kan kujerar naki don hana sanyawa Iran takunkumi.