1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

020710 Inside Europe Villepin gegen Sarkozy

July 26, 2010

Tsofan Firaministan Faransa Dominique de Villepin ya hita daga UMP ya ƙirƙiro sabuwar jam´ iya

https://p.dw.com/p/OV77
Dominique de Villepin da Nikolas SarkozyHoto: AP

Tun lokacin da Nikolas Sarkozy  ya ɗauki jagorancin ƙasar Faransa, ya fara shiga ƙafar wando guda da tsofan Firaminista na zamanin mulkin Jacques Chirac wato Dominique de Villepin, wanda ke matsayin jigo a wannan jam´iya.

Ƙiddidigar jin ra´ayin da wasu kafofin lissafi su ka shirya, na nuna cewar a yanzu Dominique de Villepin ya fi Sarkozy ƙima a idanun magoyan bayan jam´iyar UMP da ma sauran al´umar Faransa wanda su ka ƙosa da halayen shugaban.

Danganta tsakanin magabatan biyu ta yi tsami matuƙa, inda a watan da ya gabata, de Villepin ya yanke shawara ƙirkiro jam´ iyar sa da ya raɗawa suna " République Solidaire", ya kuma bayanawa ɗimbin magoya bayansa burin da ya ke buƙatar cimma:

"Mu na buƙatar girka wata jam´iya da za ta kasance mattatarar Faransawa ba tare da bambancin aƙida ko jinsi ko addini, ko kuma alƙiblar siyasa ba. A Faransa kowa ya shaidi yadda ake gudanar da mulki a yanzu tare da kura-kura masu yawa ,saboda haka ya zama wajibi a cenza."

Ga alamu dai wannan sabuwar jam´iyar ta fara samun karɓuwa ta la´akari da yadda jama´a da dama ke kira ga Dominique de Villepin ya hito takara a zaɓen shugaban ƙasar shekara 2012.

Bikin ƙaddamar da jam´iyar "République Solidaire" a watan Juni ya samu halartar dubunan jama´a birnin Paris.

To sai dai masu fashin baƙin siyasar a Faransa na hasashen cewa abin da kamar wuya Dominique de Villepin ya kai labari ko da ma ya shiga takara a zaɓen shekara ta 2012.Frederic Dabi manazarci ne  a fagen siyasar Faransa ya bada dalilai:

"Lashe zaɓe na buƙatar bataliyar yaƙin neman zaɓe mai ƙarfi.Sannan da sumun cikkaken goyan bayan jama´a.

A yanzu, de Villepin na matsayin saniyar ware a cikin  UMP.Ya na samun goyan baya daga ´yan majalisa goma kawai na wannan jam´iya.Wannan rashin cikkaken goyan baya daga wakilan al´uma, babban cikas ne gare shi , a zaɓen shekara 2012".

To sai dai a halin da ake ciki magoya bayan jam´iyar UMP na zargin shugaban ƙasar Faransa da maida jam´iyar tamkar abin mallakarsa, ya na naɗa wanda ya ga dama a matsayin da ya ga dama ba tare da yin la´akari da cencenta ba, sannan duk wanda ke nuna masa turjiya a cikin jam´iyar ,ya na ɗaukar sa a matsayin ɗan adawa.

Shi ko wannan halaye ba za su taimakawa de Villepin ba, ya taka birnin ga burin Sarkozy na zarcewa kan karagar mulki a zaɓe mai zuwa ?

Ƙiddidigar jin ra´ayin jama´a ta watan da ya gabata, ta nuna cewar de Villepin ya zarta Nikolas Sarkozy farin jini a idanun faransawa, idan ta kasance magabantan biyu su ka aje takara a zaɓen shekara ta 2012, bisa dukkan alamu wanda zai ci moriyar wannan rabuwar kanu, shine ɗan takara jam´iyar gurguzu wato PS.

To sai dai fa daga yanzu zuwa shekara ta 2012 akwai sauran tafiya, kamin nan, za a ci gaba da lisafin duna  a fagen siyasar Faransa, ko da shike hausawa na cewa "ba a san maci tuwo ba ,sai miya ta ƙare".

Mawallafi: Yahouza sadissou Madobi

Edita: Mohammad Nasiru Awal