1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a ƙasar Iraqi

April 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1o

Shugabannin siyasa a ƙasar Iraqi na cigaba da shawartawa a game da rabon manyan mukamai a sabuwar gwamnatin haɗin kan ƙasa gabanin zaman majalisar dokoki wanda zai gudana a ranar Litinin mai zuwa. Sai dai rahotanni na baiyana cewa babu alamun zaá cimma masalaha cikin hanzari. Kakakin haɗaɗɗiyar jamíyun yan sunni Zhafer al-Ani yace, ga yadda alámura ke gudana, yana da matuƙar wahala a kawo ƙarshen kiki-kaka a game da makomar P/M Ibrahim al-Jaafari. Shawarwarin da aka gudanar a baya, sun ci tura saboda kin amincewar kurɗawa da yan sunni, na tsaida Ibrahim al-Jaáfari a matsayin P/M. A waje guda kuma shugabannin jamíyun ƙawancen yan shiá, sun sanar da cewa suna ƙoƙarin cimma yarjejeniya domin maye gurbin Ibrahim al-Jaáfari da wani ɗan takarar daga cikin jamíyar sa ta Daáwa. Mai rikon mukamin kakakin majalisar dokokin Iraqin Adnan Pacaci yace suna fatan cimma yarjejeniya a yau din nan. A halin da ake ciki rukununin yan sunni sun gabatar da sunayen yan takara uku waɗanda suka haɗa da Adnan al-Dulaimi, a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, Tareq al-Hashemi a muƙamin shugaban majalisa sai kuma Khalaf al-Alyan domin riƙe mukamin mataimakin P/M.