1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a Cote D´Ivoire

August 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuEQ

Shugaban ƙasar Cote D´Ivoire Lauran Bagbo, ya bayyana yiwuwar shirya zaɓen shugaban ƙasa kamin ƙarshen wannan shekara.

A yayin da ya ke jawabi albarkacin ranar samun yancin kan Cote D´Ivoire, shugaba Lauran Bagbo, ya tabbatar da cewar, a shire ya ke, a gudanar da zaɓe a watan Desember na wannan shekara, amma tare da amincewar ɓangarorin da abun ya shafa.

A sakamakon yarjejeniyar da aka rattaba hannu kanta, a birnin Ouagadougou na Burkina Faso, tsakanin yan tawaye da dakarun gwamnati, a watan Janairu ne, na shekara ta 2008, a ka tsara shirya zaɓen shugaban ƙasar.

To amma har ya zuwa yanzu, babu alamu za a cimma wannan buri, ta l´akari da tafiyar haiwainiyar da ake fuskanta, wajen aiwatar da matakan wannan yarjejniya.

Har yanzu yan tawaye FN na cikin damara, sannan ba a fara rijistan masu kaɗa ƙuri´a ba , wanda cemma sune batutuwa 2 masu mahimmanci, da su ka hana ruwa gudu, a yunƙurin kawo ƙarshen rikicin tawayen a ƙasar Cote D´Ivoire.