1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a Isra´ila

May 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuLr

Praministan Isra´ila Ehud Olmert, na ci gaba da fuskantar matsin lamba, domin yayi murabus daga muƙamin sa, a sakamakon kura-kuran da a ke zargin sa da tabkawa, a lokacin yakin da a ka gwabza, tsakanin Isra´ila da ƙungiyar Hizbullahi ta ƙasar Libanon.

Matsin ƙaimi na baya-bayan nan, ya hito daga shugaban jam´iyar adawa, Benjamin Nitamyu.

A wata hira da yayi da gidan Redio Isra´ila, a yau litinin,Nitanyu ,ya nunar da cewa, hanya ɗaya mafi inganci, domin warware rikicin siyasa Isra´ila, itace murabus ɗin Praminsita.

Idan ba a manta a makon da ya gabata kimanin mutane dubu 100, su ka shirya zanga-zangar lumana, inda su ka buƙaci Ehud Olmert, yayi murabus.

Saidai ya zuwa yanzu, Praministan na ci gaba da yin kunen uwar shegu.