1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a kasar Cote D´Ivoire

Yahouza SadissouFebruary 2, 2006

Tawagar Afrika ta Kudu ta kammalla tantanawa da bangarorin masu gaba da juna a Cote D´Ivoire

https://p.dw.com/p/Bu1u

A kasar Cote D`Ivoire, an kawo karshen tantanawa ta yini 2, da aka yi, tsakanin tawagar shugaban Afrika ta Kudu, Tabon Mbeki, da ke shiga tsakanin rikicin kasar, da bangarori daban-daban masu gaba da juna.

Wannan sabuwar ganawa, ta maida alkibla, a kan batutuwa da su shafi majalisar dokoki, da tsare tsaren zaben da za a gudanar a karshen shekara da mu ke ciki.

Shugaban tawagar Afrika ta Kudu ,ya bayana wa manema labarai cewa, ya gamsu da masanyar ra´ayoyin da yayi;duk da yake, babu wani abun azo a gani da a aka cimma.

Shugaban Lauran Bagbo da Praminista Charles Konnan Banny, da shugabanin jamiyun adawa da masu rike da ragamar mulki, da su kansu yan tawaye, sun cimma matsaya daya ta wajibcin tsamo Cote D´Ivoire, daga halin kikki kakka da ta ke ciki, ta hanyar tuntubar juna.

A dangane da batun majalisar dokoki shugaban yan adawan Cote D`Ivoire, Allasan watara da yan tawayen sun nuna rashin amincewa da matakin da shugaba Lauran Bagbo ya dauka, na zarcewar yan majalisar, bayan karewar wa´adin su.

Kazalika su ma, yan majalisar jam´iyun adawa sun kin amincewa su zarce.

Bayan tantanawa da bangarori daban-daban masu rikici tawagar, ta sadu da wakilan Majalisar Dinkin Dunia, inda su ka yi bitar halin da ake ciki, a yunkurin maido zaman lahia a Ivory Coast.

Ta wannan fanni, sakatare Jannar na Majalisar dinkin Dunia Koffi Annan ,yayi kira ga hukumomin Cote D´Ivoire, cewa yaunin tsaran lahiyar jami´an majalisar Dinkin Dunbia,ya rataya a wuyan su.

Kiran ya biwo bayan rikicin da ya wakana a kwanakin baya, inda matasa, masu goyan bayan shugaba Lauran Bagbo, su ka kai hari, ga wasu daga membobin tawagar Majalisar Dinkin Dunia.

Annan ya kara da cewa,Komitin Sulhu nan da dan lokaci mai zuwa, zai dauki kudurin saka takunkumi ga mutanen da aka tabbatar sunyi kaurin suna, a walwale tumkar da ake don dinke baraka a Cote D´Ivoire.

Charles Ble Gude, shugaban matasa masu biyyaya ga Lauran Bagbo na sahun gaba na wanda za su fuskanci wannan hukunci.

Karshen ziyara tawagar Afrika ta kudu ,ya zo daidai da taron farko, da shugaban jam´iyar RDR Allasan Wattara, ya shugabanta, bayan dawowar sa, daga gudun hijira na tsawan shekaru 3 a kasar Faransa.

Allassan Wattara,ko kuma ADO, dan takara a zaben shugaban kasa na watan oktober mai zuwa, ya jagorancin taron kolin gudanarwa na RDR a cibiyar Jam´iyar da ke birnin Abijan.

A yayin da yake hira da manema labarai, ya nuna mattukar murna, da ganawar da yayi da magoya bayan sa.

Ya ce babban burin da jam´iyar sa, ke dauke da shi, shine na taka mihimiyar rawa, domin maido da kwanciyar hankali a cikin kasa.