1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a kasar Malawi

October 19, 2005
https://p.dw.com/p/BvOj

Majalisar dokokin kasar Malawi, ta shiga wani yunkuri na tsige shugaban kasa Bingu wa Mutharika, da ta ke tuhuma da karbar rashawa.

A wani gamen katari wannan yunkuri ya wakana a ranar da kungiyar Transpary International, ta gabatar da rahoton ta na shekara shekara, a game da cin hanci da rashawa, inda a bana ma, kasashen Afrika su ka rike matsayin su ,na sahun gaba, ta wannan mumunar dabi´a, da ke daya daga tubalin farko, na dawwamar da talauci a wannan nahiya.

Yan adawa ne, da farko su ka gabatar wa majalisa bukatar gudanar da kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasa, ta hanyar kutsa ayar doka, mai bada damar, tsige shugaban kasa idan a ka same shi da lefin cin amanar kasa.

Bayan kada kuri´a a kan wannan doka, ta samu shiga a majalisa, abinda masharahanta ke dauka, tamkar matakin farko na tsige shugaban kasar Malawi.