1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a Kote Divoire

Yahouza sadissouSeptember 1, 2005

Tabon Mbeki ya gabatar da rahoton sulhunta rikicin Kote Divoire ga Majalisar Dinkin Dunia.

https://p.dw.com/p/Bva0

A kasar Cote d´Ivoire, rikicin siyasa ya dauki wani saban sallo, bayan da yan tawaye, da yan adawa su ka bayana kauracewa zaben shugaban kasa, da a ka tsara shiryawa, ranar 30 ga watan oktober,mai zuwa, da kuma bukatar su, ta girka sabuwar gwamnnatin rikon kwarya, tare da kebe shugaban mai ci yanzu Lauran Bagbo.

Kwanaki 2, bayan wannan sanarwan shugaban kasar Afrika ta kudu Tabon Mbekin da kungiyar taraya Afrika, ta nada a matsayin mai shiga tsakani, ya gabatar da rahoton sa ga majalisar dinkin dunia, tare da bayana ajje mukamin na mai sulhunta rikicin kasar.

Ministan tsaro na Afrika ta kudu ne, Mosuioa Lekota, ya gabatar da rahoton da yawun MBeki.

Ya bayana matakai daban daban, da a ka bi, domin kussanto ra´ayoyin bangarori masu gaba da juna, ta yadda har su ka rataba hannu, a kan yarjejeniyar cimma zaman lahia, a birnin Pretoria, da kuma alkawarin da su ka dauka, na shirya zabe ranar 30 ga watan oktober, bayan sun kwance damaraun yaki.

Ministan tsaro na Afrika ta kudu ,ya tabatar, da yiwuwar shirya zaben, a lokacin da aka tsaida ka´ida, muddun bangarori daban daban, na dauke da kyawkyawar aniya, ta cimma wannan manufa..

Kwana daya, bayan matakin da ya dauka, na kauracewa shiga tsakanin, shugaban kasar Afrika ta kudu, Tabon Mbeki, a jiya laraba, ya cenza matsayi.

Ya bayanawa majalisar cewa, a shire ya ke, ya ci gaba da shiga tsakanin, amma ya na kara neman karfin gwiwa, daga kungiyar taraya Afrika, da ta dora masa, wannan yauni, da kuma ita kanta, majalisar Dinkin Dunia.

To saidai, yan tawayen FN, sun rubuta wasika, ga shugaban kungiyar taraya Afrika, Olesegun Obasanjo, inda su ka bayana cewa, ba su bukatar kwata -kwata, sulhu daga Tabon MBeki.

Sun kuma yi barazanar kai karan Afrika ta Kudu, gaban Majalisar Dinkin Dunia, bayan sun zarge MBeki, da sayar da makamai ga Lauran bagbo, duk da takunkumin da Majalisar Dinkin Dunia, ta saka, na hana sayar da makamai ga kasar Cote dIvoire.

A daya hannun kuma yan tawayen FN, sun kalubalanci ministan tsaro, na Afrika ta kudu, wanda a cewar su, ya yi kalamomi na batanci, ga kungiyar tawaye, da kuma shiga sharo ba shanu, ga al´amuran da su ka shafi Cote Divoire.

Shugaban rundunar tawaye, Guillaume Soro,ya bayana matukar bacin rai, a game da jawabin, na ministan tsaro, a Majalisar Dinkin Dunia.

Bugu da kari, wasikar, ta soki mataimakin ministan harakokin waje, na Arika ta kudu, Azizi Pahad, ta ya fito kara kara, ya zargi yan tawaye, da sa tarnaki, ga yunkunrin warware rikicin Cote Divoire.

Sun ce wannan na nuni, da ba da zuciya daya ba, shugaba Tabon Mbeki ke shiga tsakanin.

A nasa gefe, Shugaban Lauran bagbo, a jiya laraba, ya maida matani, inda ya yi watsi, da bukatocin yan tawaye, da yan adawa, na sabke shi, daga karaga mulki, ranar 30 ga watan oktober da kuma girka gwamnatin rikon kwarya.

A game da zaben shugaban kasar, Bagbo, ya bayana cewa babu shakka, za shirya shi, a ranar da a ka tanada ta farko, inda kuma har bukata daga shi, ta taso, to ba zata wuce yan kwanaki, ba, shima, bisa dalilin shirye shirye, ba na siyasa ba.

Kasar Fransa, da ke bin sau da kafa, yadda al´amura ke wakana, a kasar Cote Divoire, ta yi kira ga bangarori masu gaba da juna, da cewa, yanzu fa lokaci na su daina wasa da hankullan jama´a.

Su kuma dauki matakan aiki, da yarjejeniyoyin da su ka sa hannu a akai na shinfida zaman lahia.