1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a majalisar dokokin Ghana

December 23, 2016

'Yan majalisar dokokin kasar Ghana sun yi ta tashi baram-baram daga yawancin zaman majalisar, a sakamakon rashin jituwa da suke samu a bisa zantuttuka da dama kafin mika mulki ga sabuwar gwamnati.

https://p.dw.com/p/2UodA
Parlament in Accra, Ghana
Majalisar dokokin kasar GhanaHoto: DW/I. Kaledzi

Bangaren mara sa rinjayen majalisar dokokin dai sun ce ba za'a dama da su ba a kowace harakar majalisar dokokin sai an basu kofin takardun sauyin gwamnatin da zai kasance nan da ranar bakoye ga watan Janairu mai zuwa, inda daga lokacin jam'iyyarsu ce za ta jagoranci madafun ikon mulkin kasar. A dokance dai kuma tare da amfani da sabon kudirin dokar sauyin shugabanci, nauyin mika wa 'yan majalisa wadan nan takardu ya rataya ne a wuyan bangaren zartaswa na gwamnati amma kuma ya gaza.

Ghana Präsidentschaftswahlen- Nana Akufo-Addo
Sabon zabeben Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo Hoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Bayan wannan dai muhimmin kudirin da bangaren marasa rinjayen ke yi wa kafar ungulu shi ne na yancin samun labarai, wanda gwamnatin mai barin gado ke kokarin zartas wa gabanin sallamar majalisar, wanda gwamnatocin da suka shude suka gaza aiwatarwa. Aban Gbagbin shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin kasar ta Ghana.

"Ya kamata wannan majalisar ta rattaba wannan kudirin gabanin kawo karshen aikinta ko ta halin kaka. Na jagoranci kwamitin, kuma an kamala komai na shirye-shirye tun a shekarar 2013 kuma na gabatar wa Ministan shari'a cikakken rahoto wanda shima ya rattaba hannu. Kai wa wannan munzali kuma a sa kafa a shure ba zai misaltu da komai ba face janyowa kasar bashi."

John Dramani Mahama bei Conflict Zone
Shugaban kasar Ghana mai barin gado John Dramani Mahama Hoto: DW

Jama'a da dama ne dai ke ganin bakin alkalami ya riga ya bushe wa gwamnatin NDC mai barin gado, tare da nuna ra'ayin cewar wannan wani jinkiri ne acikin ganganci. Majalisar dai ta dage zaman na ta har ya zuwa wani mako, inda ake san ran kai wa ga cimma daidaito.