1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

October 8, 2010

Matsaloli na siyasa da taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya na neman zama ƙalubale ga shugaba Jonathan Goodluck

https://p.dw.com/p/PZT6
Shugaba Jonathan Goodluck na NijeriyaHoto: picture-alliance/dpa

Ko da yake a wannan makon ma dai halin da ake ciki a ƙasar Sudan dangane da shirye-shiryen ƙuri'ar raba gardama game da makomar kudancin ƙasar shi ne ya fi ci wa jaridun na Jamus tuwo a ƙwarya, amma kuma sun yi bitar batutuwa iri daban-daban da suka shafi nahiyar Afirka. Misali dai jaridar Süddeutsche Zeitung, wadda tayi batu a game da gurguntaccen matsayin da shugaban Nijeriya Jonathan Goodluck ke da shi a yanzu a fafutukarsa ta yin ta-zarce akan karagar mulki sakamakon harin da aka kai a daidai ranar da Nijeriya ke bikin cikarta shekaru hamsin da samun 'yancin kanta daga Birtaniya. jaridar ta ce:

Haus-Einsturz in Abuja
Taɓarɓarewar tsaro a AbujaHoto: DW

"Harin na baya-bayan nan, wani babban koma baya ne ga ƙoƙarin da ake yi na ɗinke ɓarakar da ake fama da ita a jihar Nigerdelta kuma babban ƙalubale ga shugaba Jonathan Goodluck. Akwai dai masu tababa da tabka mahawara a Nijeriyar game da ko shin ba da gayya ne aka kai wannan hari don raunana matsayin shugaba Goodluck a ƙoƙarinsa na tsayawa takarar zaɓen ƙasar da ake shirin gudanarwa shekara mai zuwa ba. Masu saka ayar tambayar dai na tattare ne da ra'ayin cewar wannan hari ba ya da wata dangantaka da rikicin Nigerdelta, wata manufa ce ta gwagwarmayar kama madafun iko a makekiyar ƙasar ta yammacin Afirka."

Niederlande Kriegsverbrechertribunal Den Haag Naomi Campbell
Naomi Campbell na ba da shaida a shari'ar Charles TaylorHoto: AP

A shari'ar da ake yi akan tsofon shugaban ƙasar Liberiya Charles Taylor ga alamu za a nemi halarcin Jeremy Ratcliffe shugaban gidauniyar taimako ta Nelson Mandela a Afirka ta Kudu domin ya ba da shaida sakamakon bayanin da 'yar gwaje-gwajen tufafin nan ta Birtaniya Naomi Campbell ta bayar a zauren shari'ar, wadda ta ce bayan kyautar damantin da Taylor yayi mata bayan liyafar cin abincin dare a gidan Nelson Mandela shekarar 1997. Tuni dai Ratcliffe ya miƙa wa mahukuntan Afirka ta Kudu damantin da ya adana a cikin wani sunduƙi a gidansa tsawon shekaru goma sha uku, bisa iƙirarin cewar bai fito da maganar fili ba ne saboda gudun ka da ya shafa wa gidauniyar ta Mendela kashin kaza, kamar yadda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rawaito.

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel ta yi sharhi ne akan rashin wata nagartacciyar ɗamara da akan yi wa rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda a ganinta shi ne ainhin musabbabin rashin taɓuka kome wajen kandagarki ko kuma tinkarar duk wata rigima ko ta'asa da ka taso, misali dai a ƙasar Kongo, inda ƙungiyoyin 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka ba tare da rundunar kiyaye zaman lafiyar ta taɓuka kome ba. Haka ma dai a lardin Darfur na ƙasar Sudan da sauran wurare da dama da ake fama da tashe-tashen hankula a cikinsu a cewar jaridar ta Der Tagesspiegel.

Kongo Indien UN Soldaten
Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a KongoHoto: AP

A cikin wani sabon ci gaba kuma jihohin Jamus na fatan canza salon kamun ludayinsu game da korar matasa baƙi da akan komar da su gida bayan samun cikakken horo a nan ƙasar, kamar yadda mujallar Der Spiege ta rawaito ta kuma ƙara da cewar:

"Wannan maganar ta fito fili ne sakamakon shirin da aka yi na mayar da Kate Amayo gida Ghana bayan da ta kammala makarantar sakandare tare da gagarumar nasara. Ita wannan matashiyar dai mahaifiyarta ce ta kawo ta nan ƙasar don zama tare da ita ko da yake ita kanta mahaifiyar ta dogara ne aka tallafi na gwamnati. Amma Kate nan da nan ta ƙware a harshen Jamusanci ta kuma samu daraja ta ɗaya a kammala sakandare. Akan fuskanci irin wannan matsalar kusan a kowace shekara. Amma abin takaici shi ne yadda sauran ƙasashe ke madalla da matasa amma ita Jamus dake korarsu bayan ta ba su kyakkyawar horo a maimakon ta ci gajiyarsu."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Halima Balaraba Abbas