1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a Senegal

August 17, 2006
https://p.dw.com/p/BumR

Ƙasar Senegal, ta shiga wani ruɗanin siyasa, a yayin da ya rage yan watanni ƙalilan, a shirya zaɓen shugaban ƙasa.

Wata kotu a birnin Dakar, ta yanke hukunci ɗaurin wattani 3, ga ɗaya daga shugabanin adawar ƙasar, wato Jean Paule Dias, bayan an tuhume shi, da ambata kalamomin da su ka yi nasaba, da hallaka shugaban ƙasa Abdoulahi wade.

Sannan kotu ta tuhume shi, da nuna shaku, ga ƙoshin lahiar shugaban ƙasar mai shekaru 79 a dunia.

Dias, ya bayana ƙarara, cewar Abdoullahi, ba zai iya jagorancin Senegal ba, har ƙarin wasu shekaru 7,muddun a ka sake zaɓen shi, a matsayin shugaban ƙasa a watan februaru mai zuwa.

Saidai lauyan ɗan adawar, ya ce za su ɗaukkaka ƙara.