1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a tsibirin Comoro

June 20, 2007
https://p.dw.com/p/BuIK

Saban shugaban tsibirin yankin Anjuwan na Komoro,Mohamed bakar, ya girka gwamnatin sa , a yau laraba, bayan zaɓen da ya ce an yi masa, ranar 10 a watan da mu ke ciki.

An rantsar da saban shugaban makon da ya gabata, saidai gwamnatin Tarayya tsibirin Komoro, da ƙungiyar taraya Afrika, sun yi wasti da wannan zaɓe, wanda su ka ce ya saɓawa tafarkin demokradiya.

Gwamnatin Taraya ta yi barazanar anfani da ƙarfin soja, domin hamɓara da shugaban Mohamed Bakar, matakin da ya samu goyan baya, daga ƙasar France ,da ta yi wa tsibirin mulkin mallaka.

daga samun yancin kan tsibirin Komoro, a shekara ta 1975, zuwa yanzu,ta fuskanci juyin mulki, ɗaya na bin ɗaya har guda 19.