1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasar kasar Nepal

April 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bv17

Dakarun gwamnati a kasar Nepal sun harba barkonon tsohuwa a kan dubban masu zanga-zanga wadanda suka bijirewa dokar hana fita don yin gudanar da zanga zangar nuna adawa da Sarki Gyanendra a birnin Kathmandu. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce an jiwa akalla mutane 80 rauni. Sannan kuma an katse hanyoyin sadarwa na wayoyin salula don hana masu zanga-zangar tuntubar juna ta wayar tarho. Kawance ´yan jam´iyu 7 da suka fara zanga-zangar sun yi watsi da alkawarin da Basaraken yayi na maido da mulkin demukiradiya. Akalla mutane 12 aka kashe sannan wasu daruruwa suka samu raunuka a tashe tashen hankulan da suka faru tun bayan fara zanga-zangar a ranar 6 ga watannan na afrilu.