1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasar kasar Zimbabwe

Zainab A MohammedMarch 12, 2007

Cafke shugabannin adawa jiya a Harare

https://p.dw.com/p/Btw2
Shugagaban Adawa a Zimbabwe Tsvangirai
Shugagaban Adawa a Zimbabwe TsvangiraiHoto: AP

Duk da matsaloli na mayar da ita saniyar ware da gwamnatin Zimbabwe ke cigaba da fuskanta daga kasashe dake makwabtaka da ita da kuma kasashen yammacin turai,akarshen makon daya gabata nedai jamian tsaro dake wannan kasa suka cafke shugaban jammiyar Adawa ta MDC,saboda shirya gudanar da wani gangami na bukatar sauyi a wanna kasa dake kudancin Afrika.

Shugaban babbar jammiiyar adawa ta MDC Morgan Tsvangirai ya sha dukan fitan arziki ayayinda yake tsare a kurkukun jamian yansandan Zimbabwe bayan cafke shi a jiya lahadi,a yunkurinsa na halartan zanga zangar adduoi na adawa da harkokin mulkin wannan kasa.

Bayan sakinsa dai sai da aka garzaya dashi asibiti domin jinyan raunuka daya samu sakamakon yadda jamian tsaron sukayi dashi.Inncent Chagonda dake4 zama lauya,ya fadawa kamfanin dillancin labaru na Reuters bayan ziyartan ofishin yansandan dake Harare cewa,da wuya ka banbanta kann shugaban adawan daga fuskarsa,saboda ko gani sosai bayayi sakamakon irin rauni da yaji,wadda ta kai ga daure kansa da bandeji.

Mrt Chagonda yace a matsayinshi na lauyan Mr Tsvangirai,bai samu sukunin magana dashi ba,kazalika sauran lauyoyinsa.Yace ya samu hangen shugaban jammiyar ta MDC ne daga nesa,ayayinda jamian yansandan ke zagayawa dashi.

Lauyan ya kara dacewa yansandan sun tabbatar dacewa sun kaishi asibiti adaren jiya,wanda shine dalilin dayasa yake daure da bandeji a akansa.

Mr Morgan tsivangirei ya shirya gudanar da wannan adduoi a dandalin taro nedai,da dadawowarsa daga ziyarar dayakai kasar Afrika ta kudu dake makwabtaka da Zimbabwe,inda ya nemi hadin kana kasashen dake makwabtaka da ita dasu basu hadin kaia a kokarinsu na ganin karshen mulkmin shugaba Robert Mugabe.

"Bazaku amince da kasar dastake kashe kanta ba,idan har kuna muradin gina kungiyar kasashen yanki da zasu kare mutuncin ku a idanun kasashen duniya.Dangane da hakane yake matukar muhimmanci ku hada kanku ,tare da magana da murya guda dangane da halin mawuyaci da kasar Zimbabwe ke ciki,nayi matukar farin ciki da ministan harkokin waje na kasar kasar Zimbawe ya furta hakan".

Wadanda suka shirya wannan gangami na aduoi,wanda kuma jamian yansanda suka hana a gudanar saboda sabawa dokar gwamnatin zimbabwe,wanda ya haramta a gudanar da gangami kowane iri har tsawon watanni uku,sun bayyana cewa Mr Tsvangirai ya some har sau uku,sakamakon irin dukan dayasha a hannun yansa kafin a gaggauta kaishi asibiti.

Bugu da kari kawo yanzu babu wanda yasan halinda sauran manyan shugabanin kungiyoyin adawa dana sakai da aka cafkesu jiya tare da shugaban Jamiiyyar ta MDC,inji lauyoyinsu,wadanda aka hanawa sukunin ganinsu.

Tsare shugaban jammiyar adawa Morgan tsivangirai wadda Amurka tayi Allah wadansa dai,yazo ne adaidai lokacin da kasar ta Zimbabwe ke cigaba da fama da matsaloli na durkushewar tattalin arziki a karkashin gwamnatin Robbert Mugabe,wanda yake jan ragamar mulkin kasar da samun yancin kai daga Britania a 1980.