1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin sojin sa kai a yankin hakan mai na Niger Delta

January 15, 2006
https://p.dw.com/p/BvCC

Wasu ´yan bindiga da ba´a ganesu ba sun yi arangama da sojojin Nijeriya dake gadin wani wurin hakan mai na kamfanin Shell dake yankin Niger Delta. ´Yan bindigan sun kai harin ne akan dandamalin hakan mai na Benisede a daidai lokacin da ake kara nuna fargaba dangane da makomar wasu baki, ma´aikatan hakan mai su 4 wadanda sojojin sakai na yankin Niger Delta suka yi garkuwa da su kwanaki 5 da suka wuce. Birgadiya-Janar Elias Zamani ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP cewa an kai harin ne da misalin karfe 7 na safe agogon Nijeriya, amma ba su san wadanda suka kai harin ba kuma kawo yanzu ba su sani ba ko rayuka sun salawanta.