1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

Tijani LawalAugust 29, 2010
https://p.dw.com/p/Oyla
Sheik Ali Mohamud Rage, kakakin ƙungiyar AlshababHoto: AP

Ko da yake dai a wannan makon halin da ake ciki a ƙasar Somaliya shi ne ya fi ɗaukar hankalin jaridun na Jamus, amma kuma sun leƙa sauran sassa na Afirka domin tsegunta wa masu karatu ire-iren wainar da ake toyawa a fannoni na siyasa, tattalin arziƙi da sauran harkokin rayuwa ta yau da kullum a sassa daban-daban na wannan nahiya...Da farko dai zamu fara ne da rahoton Jaridar Süddeutsche Zeitung ta bayar dangane da mummunar ɗai'ar nan ta yi wa mata fyaɗe a wuraren da ake fama da yaƙi a cikinsu tana mai ba da misali da rahoton da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayar a game da dubban-dubatar matan da aka yi wa fyaɗe a ƙasar Kongo. Jaridar ta ce:

Tanklasterunglück im Kongo
Dubban-dubatar mata ake wa fyaɗe a ƙasar KongoHoto: AP

"Ba wanda ke ba da la'akari da wannan mummunar ta'asa, inda galibi masu alhakin lamarin kan tsira ba tare da wani hukunci ba. Ta'asar fyaɗen ta baya-bayan nan dai ana zargin mayaƙan ƙungiyar Mai-Mai da dakarun sa kai na FDLR ne da laifin aikatawa, waɗanda suka mamaye yankin Luvungi tun daga 30 ga watan yuli zuwa uku ga watan nan na agusta, amma kuma Majalisar Ɗinkin Duniya tayi iƙirarin cewar sai a ranar 12 ga wata ne ta samu labarin ta'asar fyaɗen. Gasba ɗaya dai alƙaluman majalisar sun nuna aikata ta'asar fyaɗe ga mata dubu takwas a shekarar da ta gabata ko kuma mata sama da dubu 100 tun bayan ɓarkewar yaƙin Kongo a shekara ta 1996."

A halin da ake ciki yanzun yaƙin Somaliya ya ɗauki wani sabon salo inda mayaƙan ƙungiyar Alshabab mai zazzafar aƙida dake kuma samun goyan-baya daga wasu dakarun mayaka daga ƙasashen ƙetare suka fara ɓar da kama don kai hare-harensu na ƙunar baƙin wake kamar yadda ya faru a wannan makon a birnin Mogadishu, a cewar jaridar Neues Deutschland. Jaridar ta ƙara da cewar:

"Manufar ƙungiyar ta Alshabab ita ce ta fatattaki raunanniyar gwamnatin riƙon ƙwarya ta Somaliya dake samun goyan baya daga ƙasashen yammaci da kuma kariya daga sojojin kiyaye zaman lafiya na Ƙungiyar Tarayyar Afirka da aka tsugunar a Mogadishu. Ita dai Somaliya tun abin da ya kama daga shekarar 1991 ba ta da wata tsayayyar gwamnati kuma tana daɗa durmuya a cikin yamutsi. A sakamakon haka manazarta ke yin kira ga kafofi na ƙasa da ƙasa da su sake bitar manufofinsu dangane da ƙasar ta Somaliya."

Somalia Shebab Miliz Angriff auf Hotel in Mogadischu
Harin 'yan Alshabab a Hotel Muna dake MogadishuHoto: AP

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung sharhi tayi tana mai cewar:

"Somaliya dai tuni ta wargaje kuma maƙobciyarta a ɗaya ɓangaren na gaɓar tekun baharmaliya, wato ƙasar Yemen, ita ma dai tana fuskantar irin wannan ƙaddara. 'Yan ta'adda na ƙasa da ƙasa suna da cikakkiyar dama ta cin karensu babu babbaka a dukkan ƙasashen biyu. Kuma a haƙiƙa suna samun goyan baya daga sauran al'uma ne saboda ƙasashen yammaci ba su bin manufofi na gaskiya tsakani da Allah, inda galibi suka gwammace ganin an ci gaba da yaƙe-yaƙe a maimakon wata ƙungiya mai tsattsaurar aƙida ta kama ragamar mulki ko ba da goyan baya ga mulkin kama karya akan fafutukar neman ikon cin gashin kan al'uma kuma hakan ta sanya har yau ake lalube a cikin duhu wajen neman bakin zaren warware rikicin ƙasar Somaliya."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu