1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Taiwan da Sin

Zainab A MohammadMay 6, 2005

Ziyarar shugaban jammiyar adawa ta PFP ta Taiwan a kasar Sin

https://p.dw.com/p/Bvc7
Hoto: AP

Shugaban jammiyar adawa dake Taiwan James Soong yace babu yadda dangantaka zata yanke tsakanin tsibirin Taiwan da Sin,idan akayi laakari da dangantakansu mai dogon tarihi.

Shugaban Jammiyar yan adawa James Soong yayi wannan furucin lokacin daya kai gaisuwar ban girma wa Basaraken Sin na farko Qin Shi Huanghi,aziyarar kwanaki 9 dayakeyi a wannan kasa.Yace Sin da Taiwan sun rabu tun cikin ashekaru 100 da suka gabata ,kana suka dauki shekaru 50 na rashin jituwa,wanda bai dace ba.

Mr Soong yace yana da muhimmanci a koma tarihi da irin dangantaka dake tsakanin kasashen biyu tun farko,hakan ne zai tunatar da tushen wannan rikicin,wanda zai kasance abu mai sauki a kawo karshensa.

Tun daga shekara ta 1949 nedai tsibirin Taiwan ke gudanar da mulkin kanta,sakamakon tserewa da dakarun Kuomintang sukayi da dakarun Commusancin Sin zuwa nan akarshen yakin duniya.Amma Sin har yanzu na laakari dacewa tsibirin Taiwan na karkashita,kuma dole ne su hade,koda da karfin soji ne.

Gwamnatin Beijing dai bata amince da shugaba chen Shui-bian na Taiwan daya lashe zabe a shekarata 2000 da shekarata 2004 ba kan cewa Taiwan ta samu yancin kai,tare da watsi da shugaban yayi da sarrafa makamai masu linzami da Sin keyi da nufin haran wannan tsibiri.

Dangantakla dai yayi tsami tsakanin makwabtan biyu sakamakon dokar da Beiging ta zartar a watan maris,wanda ke halaltawa dakarun kasar izinin mamayar Taiwan,idan har tayi kokarin hakikance yancin kanta a hukumance.

Mr Soong dake jagorantan jammiyar PFP,yasha kira dangane da bukatar laakari da tarihinsu da aladu dasuke dashi guda,wajen dinke wannan baraka da suke fama da ita shekara da shekaru.Bugu da kari ya nuna adawa da bawa Taiwan yancin kai.

A cigaba da ziyar dayake a wannan kasa,a mako mai zuwa ne zai gana da shugaba Hu Jintao a Beijing.

Wannan ziyara tasa tazo ne ,bayan ziyarar da shugaban babbar jammiyar adawa ta KMT dake Taiwan,Lien Chan ya kai Beijing inda ya gana da shugaba Hu da jammiyar yan Kommunist dake mulkin wannan kasa,ganawar dake zama na farko tun cikin shekaru 60 da suka gabata.

Mr Soong yayi wadannan furuci nasa ne saoi kalilan bayan da shugana George W Bush na Amurka ya jaddadawa shugaba Hu bukatar komawa teburin sulhu da zababbiyar gwamnatin Taiwan.

A hiran da sukayi ta wayan tangaraho a daren jiya Bush da Hu sun tattauna matuka gaya dangane da yadda zaa warware rikicin bangarorin biyu.