1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin tattali ya ritsa da Zambia

July 14, 2009

Ƙasashe matalauta a Afirka na fama da matsalolin tattali

https://p.dw.com/p/IpDB
Shugaba Rupiah Banda na ZambiaHoto: AP

Ana iya cewar ɗaukacin ƙasashen Afrika sun samu nasarar kasancewa nesa daga matsalar tattalin arziki da duniya ta faɗa ciki na tsawon lokaci a fakaice. Hakan ba zai kasa nasaba dacewar, a mafi yawa daga cikin ƙasashen, al'ummominsu na fama da rayuwa na hannu baka hannu kwarya. Amma nazarin baya-bayannan da masana harkokin tattalin arziki suka yi, ya nunar dacewar a yanzu haka kasuwannin hada-hadan nahiyar sun faɗa cikin hali matsananci.

Babban damuwan shine yadda wannan matsalar tafi ritsawa da matalauta daga cikin su. Misalin irin waɗannan ƙasashe da rikicin tattalin ya ritsa da su ita ce Zambia, wadda ke da faɗin ƙasa da ta ninka Jamus sau biyu da yawan al'umma miliyan 12.

Zambia dai ƙasa ce matalauciya. Tana dogaro ne kacokan kan albarkatunta na tagulla da take fitarwa zuwa ƙasashen ƙetare.

Maisfeld in Sambia
Gonar MasaraHoto: DW

Farashin tagullan dai ya ruguje daga Euro 7000 tone guda, zuwa 2500. Hakan ya janyo martanin gaggawa ta ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu dake tono tare da sarrafa tagullan.

Daga cikin irin martanin kuwa har da koran mafi yawa daga cikin ma'aikatansu. Hakan ya mayar da Zambia ƙasa ta farko da ma'aikatanta suka kasance cikin hali mawuyaci na rayuwa. Dole ne sauran ma'aikatan da suka rage su yi aikin karɓa-karɓa na sa'oi 12. Amma har yanzu ma'aikatan tonon ma'adinan na samun albashin kwatankwacin euro 280 a wata, a yayin da wasu Zambiyawan ke karɓan kwatankwacin euro 40.

Hakan ya sanya mafi yawa daga cikinsu dogaro akan 'yan uwa da abokan arziki wajen samun abubuwan biyan buƙatu na rayuwa. Kamar yadda wata ɗan Zambiyan ya shedar...

15.06.09 DW-TV Global 3000 Sambia Kupfer
Haƙar Ma'adinai

"Tace bana jin daɗi ko kaɗan, domin muna cikin hali mawuyaci na rayuwa, domin muna dogaro ne wajen roko domin samun abinci, ko kuma abubuwa kamar dankali mai zaƙi domin kalacin safe. Idan kana da abokinka wanda kuke shiri sosai zai iya taimaka maka da 'yan kuɗaɗe domin biyan wasu buƙatu"

Wasu kuwa sukan gwammace zama ne akan tituna suna ihu ko kuma surutai da ƙarfi, duk da cewar sun san hakan bai dace ba kuma ba zai magance komai ba.

"Mun kasa rayuwa saboda tsadar kayayyakin abinci, da man petur, ko da farashin ya sauka ba zai amfanemu ba"

Daura da waɗannan wahalhalu kuma akwai matsalar farashin Tagulla. Buƙatu na kasuwannin Duniya na daɗa ƙaruwa. Ba wai a nahiyar Turai kaɗai ba, amma har da ƙasar Sin, domin dukkan masana'antun na buƙatar makamashin Gas. Amma a dukkan wannan yanayi, amma a ɓangaren Zambia ba ta samun wata moriya ta azo a gani.

Zambia dai ƙasa ce mai arziki, bisa la'akari da albarkatun ƙasa da take da shi. Sai dai bayan Tagulla da take da shi, Nama ne kaɗai ƙasar take fitarwa waje.

Duk da cin moriya da ƙasashe kamar Sin suke yi daga albarkatun Zambia al'ummomin ƙasar na cigaba da kokawa, saboda gwamnatin ƙasar ta gaza yin komai na ceto su daga wannan wahala.

Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Mohammad Nasir Awal