1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin tawaye a Jamhuriya Demokradiyar Kongo

December 8, 2005
https://p.dw.com/p/BvHS

Tawagar Majalisar Dinkin Dunia a Jamhuriya Demokradiyar Kongo, ta bayana damuwa a game da yadda tashe tashen hankula ke daga kamari, a yankin Katanga, dake kudu maso gabacin kasar, a sakamakon yake- yake tsakanin yan tawayen Mai-Mai da dakaraun gwamnati.

Daga farkon watan november da ya wuce ya zuwa yanzu karuwar rikici a yankin ,ya cilastawa a kalla mutane dubu 25 kauracewa matsugunan su, domin shiga gudun hijira.

A baki daya ya zuwa yanzu kimanin mutane dubu 100 su ka bar wannan yanki.

Gwamnatin Jamhuriya Demokradiyar Kongo, ta bayyana aniyar ta, ta karewa kwata kwata, da yan tawayen kudu masu gabancin kasar, kamin zabuka masu zuwa,abinda ya kara saka mutane cikin halin zullumi.