1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afrika A jaridun Jamus

August 4, 2009

A wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar hankali akan kashe-kashe na gilla da 'yan ƙungiyar Boko Haram suka aikata a Nijeriya

https://p.dw.com/p/J3Gl
´Yan ƙungiyar Boko Haram da aka kama a MaiduguriHoto: AP

A wannan makon mai ƙarewa dai ko da yake jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni da dama akan al'amuran nahiyar Afurka, amma kashe-kashe na gilla da 'yan ƙungiyar Boko Haram suka aikata shi ne ya fi ɗaukar hankalin jaridun, inda kusan babu wata jarida ta ƙasar da ba ta tofa albarkacin bakinta akan wannan mummunar ta'asa ba. A cikin nata sharhin jaridar Frankfurter Allgemeine zeitung cewa tayi:

"Wannan dai ba shi ne karon farko da ƙungiyar "Boko Haram" mai kiran kanta wai ƙungiyar Taliban ta kai farmaki na ba gaira ba dalili ba. Domin kuwa a shekara ta 2004 sai da suka kai hare-hare kan tashoshin 'yan sanda a jihohin Yobe da Borno. Sannan a shekara ta 2007 suka sake kai wani farmakin kan wata tashar 'yan sanda a Kano. To sai dai kuma kawo yanzu babu wasu tabbatattun bayanai dake nuni ga dangantakar ƙungiyar mai iƙirarin fafutukar yaɗa musulunci tsantsa a duk faɗin Nijeriya da ƙungiyar 'yan ta'adda ta Al-Ƙa'ida."

Nigeria
Hoto: AP

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung tayi tsokaci ne da muhimmancin zaman lafiyar Nijeriya da makomar zaman lafiya da kwanciyar hankali ga yammacin Afurka baki ɗaya ta kuma ƙara da cewar:

"Musabbabin ire-iren wannan rikici na addini dake addabar Nijeriya ba kome ba ne illa rashin adalcin mahukuntan ƙasar. Gwamnatin Nijeriya ta gaza wajen yaƙi da matsalar cin hanci da danniya. Muddin ba a magance wannan matsala ba da wuya Nijeriya ta samu kwanciyar hankali."

A nata sharhin jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Wannan rikicin ya zo ne a daidai lokacin da Nijeriya ke fama da ƙaƙa-nika-yi. Domin kuwa a can kudancin ƙasar dake da arziƙin man fetur, ƙungiyar tawaye ta MEND dake hana ruwa gudu ga ayyukan haƙan man tana ci gaba da fatali da tayin afuwa da gwamnati ta gabatar, a yayinda gwamnan jihar ke barazanar rufa wa MEND baya saboda ya hana wanzuwar wata sabuwar doka ta mai da aka zayyana."

Bildergalerie Ruanda Versöhnung Bild 6
Kantuna a tsakiyar birnin KigaliHoto: James Nzibavuga

A wannan makon an gano mafakar shugaban ƙungiyar FDLR, wanda ke ɗaya daga cikin masu alhakin kisan kiyashin Ruwanda da kuma ta'asar kashe-kashe na gilla dake faruwa a ƙasar Kongo a garin Mannheim dake nan Jamus. Bisa ga alamu Ignace Murwanashyaka na jan akalar dakarunsa ne ta wayar tarho a cewar jaridar Die Zeit, wadda ta ci gaba da cewar: Wannan ɗan ta kife sai da yayi shekaru yana mai dogaro akan tallafin gwamnati kafin a fallasa asirinsa."

IT für Schulkinder im Senegal
Yaran makaranta a SenegalHoto: picture-alliance / Godong

Ƙasar Senegal na daga cikin ƙasashe masu bin mulkin demoƙraɗiyya a nahiyar Afurka, amma a yanzu tana fuskantar barazana sakamakon matsalar talauci dake addabar al'umar ƙasar in ji Jaridar Rheinischer Merkur. Jaridar ta ce an fi ɗora laifin hauhawar farashin kayan masarufi da guje-gujen hijira na matasan ƙasar akan shugaba Abdoulaye Wade, wanda ake zargi da kashe maƙudan kuɗi don karɓar baƙoncin taron ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Larabawa a Dakar a shekarar da ta wuce.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal