1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin ´yan takife a yankin Niger Delta na Nijeriya

January 29, 2006
https://p.dw.com/p/BvAL
Wasu ´yan bindiga a Nijeriya sun afkawa ofishin wani kamfanin hakan mai na kasar KTK dake yankin Niger Delta mai fama da rikici, inda suka yi awan gaba da kudi sama da dala dubu 300. Kamar yadda ´yan sanda suka nunar wannan harin na daga cikin hare hare da tashe tashen hankula da ake fama da su a wannan yanki a kwanakin nan. ´Yan bindiga wadanda suka yi amfani da kanan kwale kwale masu gudun gaske sun kutsa cikin ofishin kamfanin Daewoo a jiya asabar kafin su yi awan gaba da dala dubu 307. Wata mai magana da yawun ´yan sanda ta ce ba wanda aka yiwa rauni a wannan fashi. To amma ´yan sanda na gudanar da bincike ko wannan harin wani aiki ne na ´yan takifen kabilar Ijaw wadanda suka yi garkuwa da wasu baki ma´aikatan mai su 4 kwanaki 18 da suka wuce. Tashe tashen hankulan ya gurgunta kimanin kashi 10 cikin 100 na harkar samar da man fetir a tarayyar Nijeriya.