1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin yankin Darfur na kara rincabewa

Mohammad Nasiru AwalNovember 4, 2004
https://p.dw.com/p/Bvev
´Yan gudun hijira a Darfur
´Yan gudun hijira a DarfurHoto: AP

A cikin rahoton baya-bayan nan da ya bawa kwamitin sulhu na MDD dangane da halin da ake ciki a yankin Darfur, sakatare janar na MDD, Kofi Annan ya nunar da cewa ana kara kai hare-hare a daidai lokacin da bangarorin dake yakar juna ke kokarin mayar da wasu yankuna karkashin ikonsu. Mista Annan ya ce yanzu haka wata sabuwar kungiyar ´yan tawaye ta kunno kai, kana kuma babu wani ci-gaba da aka samu wajen kwance damarun sojojin sa kai. A saboda haka kwamitin sulhu na MDD mai membobi 15 yana nazarin daukar tsauraran matakan gaggawa don ganin an aiwatar da dokokin da ya zayyana a cikin kudurorin da ya zartas da farko.

Kudurorin kwamitin sulhun dai sun yi barazanar kakabawa gwamnatin Sudan takunkuman karya tattalin arziki ciki har da na hana mata sayar da man fetir din ta a ketare, idan ta ki cika alkawuran da ta dauka na kawo karshen hare-haren rashin imani da sojojin sa kai na larabawan janjaweed ke kaiwa fararen hula, kana kuma ta gurfanad da su gaban shari´a bisa aikata laifukan yaki da kuma keta hakkin dan Adam. Annan ya ce wani taron kwamitin sulhu da zai gudana a birnin Nairobin din Kenya a ranakun 18 da 19 na wannan wata na nuwamba zai tattauna game da matakan da za´a dauka nan gaba.

Rahoton na mista Annan ya yi nuni da cewa ana samun tafiyar hawainiya wajen girke dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar TA a yankin na Darfur.

Shi kuwa jakadan Amirka a MDD John Danforth cewa yayi yana sa rai taron na birnin Nairobi zai bawa bangarorin biyu taimakon da ya kamata maimakon a yi barazanar sanya musu takunkumi. Shi kuwa kakakin ma´aikatar harkokin wajen Amirka a birnin Washington Richard Boucher nuni ya yi da cewa sake hada kann dubban sojojin sa kai Larabawa a wasu yankuna na yammaci da kudancin Darfur bayan garkuwa da mutane 18 da ´yan tawaye suka yi, wata shaida ce cewar dukkan sassan dake yakar juna ba su da niyar wanzar da zaman lafiya tsakaninsu.

Rikicin yankin Darfur, wanda MDD ta ce shine mafi muni a wannan zamani da muke ciki, ya barke ne a cikin watan fabarirun shekara ta 2003 lokacin da ´yan tawaye suka fara yakar gwamnatin birnin Khartoum, bisa dalilan cewa ta mayar da yankin saniyar ware. ´Yan tawaye na zargin gwamnati da bawa larabawa sojojin sa kai makamai, inda suke cin karensu ba babbaka akan bakaken fatun wannan yanki a wani mataki mai kama da tsabtace jinsi.