1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin yankin Darfur

September 18, 2006
https://p.dw.com/p/Buj6

Ƙasashe da ƙungiyoyi daban daban na dunia, na ci gaba da matsa lamba ga gwamnatin Sudan, domin ta amince da dakarun shiga tsakani na Majalisar Ɗinkin Dunia, a yankin Darfur da ke fama da rikici.

Ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani adama, a ƙalla 30, sun shirya zanga- Zanga jiya, a ƙasashe da dama na dunia, domin jawo hankullan jama´a agame da ta´asar da ke gudana a Darfur, inda dakarun Djandjawid, ke ci gaba da aikatata kissan gilla, ga talakawa bayin Allah, wanda ba su san hawa ba, balle sauka.

Praministan Britania, Tony Blair, ya aika da wasiƙa zuwa ga sauran shugabanin ƙasashen ƙungiyar gammaya turai, inda ya gayyace su, ɗaukar matakin da ya dace, cikin gaggawa, domin kawo ƙarshen rikicin Darfur.

A nata ɓangare yau ne, ƙungiyar tarayya Afrika zata mahaura a birinin New York, a game da zarcewa ko kuma janye dakarun ta dubu 7, daga Darfur, a ƙarshen watan da mu ke ciki.

Tun watan Ogust da ya wuce, komitin sulhu na MDD ya kaɗa ƙuri´ar amincewa da aika dakaru kimanin dubu 20, wanda za su maye gurbin sojojin AU, amma gwamnatin Khartum ta nuna adawa da wannan mataki.

Toi saidai a halin da ake ciki, an samu ɓaraka tsakanin shugaban ƙasa Omar El Beshir, da mataimakin sa Salva Kiir, wanda ya bayyana mahimmancin aika rundunar shiga tsakanin a Darfur.