1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin yankin Darfur

May 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bv05

Wakilin ƙungiyar taraya Afrika Salim Ahmed Salim, da ke jagorancin taron sulhunta rikicin yankin Darfur, a birnin Abuja na tarayya Nigeria ya bayyana ƙara wa´adin kwanaki 2, don cimma bakin zaren warware wannan rikici.

Jiya ne, shabiyun dare, wa´adin da kungiyar tarayya Afrika, ta baiwa ɓangarorin ya kawo ƙarshe, ba tare da cimma burin da aka sa gaba ba.

Tun ranar 10 ga watan Aprul, AU tare da amincewar Majalisar Dinkin Dunia,, ta gabatar da tsarin taswira shinfiɗa zaman lahia, ga ɓangarori daban daban masu gaba da juna a yankin Darfur.

Ta saidai yan tawayen, sun bayana ƙarara cewar ba za su sa hannu ba, ga wannan taswira, a yayin da wakilan gwamnatin Sudan su ka ce, a shirye su ke, su rattaba masa hannu, domin kawo ƙarshen wannan yaƙi, da ya zuwa yanzu, ya hadasa mutuwar mutane dubu 180.

Kakainn yan tawayen darfur ya gita wasu sharuda kaminamincewa da taswirar.

Shuagaban hukumar zartaswa ta AU, Alfa Omar Konare, ya bayyana matukar damuwa, a game da rashin cimma daidaito, ya kuma sanar cewa, kungiyar za ta taron gaggawa, domin ɗaukar sabin matakan da su ka cencenta.

A dangane da wannan rikici, dubun dubunan jama´a, a ƙasar Amurika, sun shirya zanga zanga ranar jiya asabar, domin jawo hankullan al´ummomin dunia a kan ta´adin da ke wakana a yankin Darfur.