1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin yankin Darfur

August 24, 2010

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi suka ga hare-haren da ake kaiwa 'yan gudun hijra a yankin Darfur

https://p.dw.com/p/Ouao
Hoto: picture-alliance/ dpa

Kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi Allah wadai da jerin hare - haren da ake ƙaddamarwa akan ma'aikatan agaji a yankin Darfur na ƙasar Sudan wanda ke fama da rikice - rikice. Kwamitin sulhun ya ambaci bada kulawa ta musamman ga sansanin 'yan gudun hijra na Kalma, tare da ƙwance ɗamarar mayaƙan sa kai da ke ɗauke da makamai domin baiwa ma'aikatan agaji sukunin yin aikin su cikin lumana.

Sau da dama dai makamai da kuma ƙungiyoyin 'yan ta kife kan bayyana a sansanonin kula da 'yan gudun hijrar, lamarin da ala - tilas kan sa ma'aikatan agajin barin wurin. Yaƙin basasar daya ɓarke a yankin Darfur na ƙasar Sudan tun cikin shekara ta 2003 ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 300,000.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Abdullahi Tanko Bala