1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin yankin palasdinawa

Zainab A MohammedOctober 4, 2006
https://p.dw.com/p/Btxt
Kungiyar Hamas
Kungiyar HamasHoto: AP

Wasu yan bindiga dadi guda sun harbe daya daga cikin shugabannin kungiyar Hamas mai mulki a yanikn palasdinu,adaidai lokacin da yake barin masallaci da safiyar yau,a gabar yamma da kogin jordan.

Wannan kisan gilla da akayiwa daya daga cikin shugabannin na Hamas yazone yini guda bayan yan jamiyyar adawa ta Fatah dake yankin palasdinawan sunyi baraszanar kashe manyan jamian kungiyar ta Hamas.

Wannan sabon rikici wanda ya barke tsakanin jamiiyu guda biyu daga gaba da juna,ya barke ne adaidai lokacin da sakatariyar kula da harkokin ketare na Amurka Condoleeza Rice ke rangadin aiki a yankin na gabas ta tsakiya,kana a daya hannun tsaka tsakin rikicin madafan iko tsakanin kungiyar Hamas mai mulki da jammiyar fatah ta shugaba Mahmoud Abbas,wanda ake gudun zai iya haifar da yakin basasa a yankin Palasdinawan.

Ayanzu haka dai Condoleeza Rice ta isa kasar Izraela bayan gabawarta da shugaba Mahmuod Abbas a yankin na Palasdinawa.Jakadar Amurkan dai tayi kira adangane da kawo karshen rikicin cikin gida daya kashe mutane 12 a wannan makon ,ayankin na palasdinawa.

Aganawar datayi a daren jaya da jamian kasashen Larabawa a birnin Alkhahiran Masar dai,Rice ta jadda muhimmancin gano bakin zaren warware rikicin dake tsakanin palasdinu da Izraela.

Wadanda suka ganewa idanunsu,harin nayau dai sun bayyana cewa,wasu mutane guda uku dauke da bindigogi cikin wata mota,a kauyen Hableh dake gabar yamma da kogin Jordan,sun harbe Mohammed Odeh mai shekaru 37 da haihuwa,adai dai lokacin da yake barin masallaci bayan sallar Asubahi.

To sai dai tuni jamian Kungiyar Fatah dake garin Qalqilya,dake makwabtaka da Hableh,suka janye kansu daga zargin wannan kisan gillan,inda suka danganta da Izraela,ayayinda a hannu guda kuma jamian Hamas dake yankin ,suka sanar dacewa basu da masaniya adangane da wadanda keda alhakin wannan harin.

To sai dai wadanda suka ganewa idanunsu,sun hakikance cewar motar dake dauke da yan bindiga dadin nada lambar kasar Izraela,domin ba safai akanga motoci da irin wannan lamba a yankin Palasdinawan ba.

Harin na safiyar yau dai yazo ne yini guda bayan rundunar mayakan Fatah,watau Al-Aqsa Brigade ,sunyi barazanar kashe manyan jamian Hamas,acikin wata sanarwa da suka gabatar.

Ayau din dai shugaban yan majalisar Fata,Azzam al-Ahmad,ya karyata wannan sanar,tare da bayyana ta kasancewa shiri ne kadai,amma kakakin rundunar Al aqsa dake Gaza,ya hakikance cewa sune suka bada sanarwar.

Fadan cikin gida daya barke a zirin Gaza da Gabar yamma da kogin jordan a wannan makon dai,namai kasancewar mafi munin zubar da jini,da yankin palasdinawan ya fuskanta ,da kirkiro shi a shekara ta 1994,akarkashin yarjejeniyar wucin gadi da aka cimma da izraela.

Wannan rikicin ne kuma a halin yanzu ya dasa ayar tambaya adangane da yiwuwar nada gwamnatin hadaka tsakanin Fatah da Hamas a wannan yankin .