1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Zirin Gaza na kara rincabewa

July 11, 2006
https://p.dw.com/p/Buqt
Rundunar sojin Isra´ila na ci-gaba da kai hare hare ta sama akan Zirin Gaza, inda jiragen saman yakinta suka yi lugudan wuta akan wata gada da kuma wuraren sojojin sa kai na Falasdinawa dake arewacin yankin. Da farko Isra´ila ta ba da sanarwar fadada farmakin wanda ta faro kimanin makonni biyu da suka wuce. Gidan radiyon sojin Isra´ila ya rawaito FM Ehud Olmert na cewa rundunar ta hada kawunan daruruwan dakaru da tankokin yaki don kutsawa sosai cikin yankin. A yau majalisar zartaswar Isra´ila zata yi wani zama na musamman inda zata tattauna game da sabbin matakan da za´a dauka da nufin kwato sojin ta da Falasdinawa ´yan gwagwarmaya suka yi garkuwa da shi a ranar 25 ga watan yuni. Yanzu haka dai daukacin mazauna Zirin Gaza sun shiga cikin wani mawuyacin hali maras misaltuwa sakamakon farmakin na Isra´ila. Jami´in gwamnatin Falasdinu Saeb Erekat yayi kira ga Isra´ila da ta kawo karshen wannan matakin karfi da take dauka.