1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rishin tabbas kan zaben shugaban kasa a Kenya

Salissou Boukari MNA
September 17, 2017

Masana siyasar kasar Kenya na aza ayar tambaya kan yiwuwar zaben shugaban kasar a ranar 17 ga watan Oktoba, bayan da kotun kolin kasar ta soke zaben sakamakon manyan kura-kurai.

https://p.dw.com/p/2k8O1
Kenia - Wahlen - Vorsitzender des Independence Electoral and Boundaries Commission Wafula Chebukati bei Pressekonferenz
Shugaban hukumar zaben kasar Kenya Wafula Chebukati yayin taron manema labaraiHoto: picture-alliance/AP Photo/S. A. Azim

Kwararru dai na nuna shakku kan lamarin idan aka dubi yadda fadace-fadace na siyasa da sauran rudanin da ake fuskanta da ke mayar da hannun agogo baya kan batun shirya zaben. A halin yanzu dai lokaci na ci gaba da kurewa, inda ta kamata 'yan kasar ta Kenya su koma ga runfunan zabe a ranar 17 ga watan Oktoba, bayan da kotun kolin kasar ta soke zaben da ya gudana sabili da manyan kura-kuran da aka tafka a zaben da aka yi na ran takwas ga watan Augusta da ya gabata. Tuni dama 'yan adawar kasar suka ce za su kaurace wa zaben muddin dai aka ki aminta da bukatun da suka gabatar na gyara a hukumar zaben kasar, wadda har yanzu ba a cike gurbin wasu wakillanta da dama da suka yi murabus ba.