1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Romano Prodi ya koma mukamin sa na Praminista.

February 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuRC

Shugaban kasar Italiya Giorgio Napolitano ya mayar da Prain-Minista Romani Prodi akan tsohon mukamin sa da ya bari farkon wannan mako, domin ya sake fuskantar wani zaben da zai tabbatar da cancantar sa na jan ragamar mulkin kasar a matsayin Prain-Minista. Shugaba Napolitano ya sanar da hakan yau da safe, bayan tattaunawa na kwannaki biyu tsakannin sa da mayan ‚yan siyasa da jami’an majalisu da suka tabbatar da goyan bayan su ga Prain-Ministan. Prodi ya tayar da guguwar rikicin siyasa a kasar ranar laraba, lokacin da ya sanar da cewar ya ajiye mukamin sa na Prain-Minista, bayan ya kunyata jam’iyar sa. Shugaban kasar Italy Giorgio Napolitano, yace ya kasa samun goyan baya ne daga majalisat dattijai akan shirin sa na aiwatar da wasu muhinmman canje canje ga al’amuran gwamnati, kara fadada sansanonin sojojin Amurka dake Vicenva, kana da kara wa’adin aikin dakarun sojin kasar dake tsugunne a Afghanistan.