1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudanin siyasa a kasar Haiti

Salissou BoukariJune 14, 2016

Ofishin Firaministan kasar Haiti ya sanar da ayyana dokar hana fitan dare daga daren Litinin zuwa wayewar wannan Talata domin rigakafin tadda zaune tsaye.

https://p.dw.com/p/1J67P
Haiti Präsident Jocelerme Privert mit Premierminister Fritz Alphonse Jean
Hoto: picture alliance/AP Images/D. N. Chery

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan adawan kasar suka kira magoya bayan su da yin kwanan zaune na nuna kishin kasa, a wani mataki na nuna kawo karshen mulkin shugaban rikon kwaryar kasar da wa'adin mulkin sa ya kawo karshe. Sai dai sanarwar ta gwamnatin ta Haiti da aka wallafa ta jim kadan kafin lokacin soma aikin dokar hana fitan, ta ce daukan wannan mataki dai ya biyo bayan samun wasu bayannai na sirri da ke cewa akwai yuyuwar yin amfani da wannan dama domin tadda zaune tsaye.

An dai haramta duk wata zirga-zirgar mutane, ko ta ababan hawa a dukannin titunan biranen kasar sai dai motocin 'yan sanda, da kuma na agajin gaggawa. Kasar ta Haiti dai ta tsunduma cikin wani yanayi na rikicin siyasa tun bayan da aka soke tsarin harkokin tafiyar ta zabukan kasar a watan Janairu da ya gabata.