1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudanin siyasa a kasar Libanon

Hauwa Abubakar AjejeDecember 4, 2006

Rundunar sojin kasar Lebanon ta kara jibge dakarunta a birnin Beirut yau litinin,saboda tsoron kada zanga zangar kin jinin gwamnati ya koma na darikun addini,bayan kashe wani dan shia da akayi cikin zanga zangar..

https://p.dw.com/p/BtxE
Hoto: AP

Wannan shine hasasar rai na farko da aka samu tun fara zanga zangar a ranar jumaa wanda ake tsoron zai koma zuwa wani yakin basasa kuma a kasar.

Majiyoyin tsaro sun baiyana cewa an kara yawan sojojin ne a yankunan yan sunni inda masu zanga zangar yan shia suka bi don kaiwa ga tsakiyar birnin Beirut a zanga zangar da sukeyi na neman kifar da gwamnati.

A yau litinin kwana na uku na zanga zangar bankuna da wuraren kasauwanci da dama sun kasance a rufe a birnin Beirut.

Yan kasuwa sunce ci gaba da rufe wadannan wurare zai rusawa wasu kasuwancinsu tare kuma da tilasata rage yawan maaikata a wasu wuraren.

A halin yanzu dai sakataren kungiyar kasashen larabawa Amr Moussa yayi gargadin cewa wannan rikici zai iya kara munanta haka kuma yace ya tattauna da jamian kasar Lebanon game da hanyoyin da zaa shawo kan lamarin,a ziyara da ya kai na saoi 24.

Amr Moussa wanda ya gana da shugabannin Lebanon da jamian kungiyar Hezbollah yace kasashen larabawa ba zasu sa ido kawai suna ganin abubuwa suna tabarbarewa a Lebanon ba.

Gwamnatin Siniora dai tana samun goyon bayan kasashen yamma da ma kasashen larabawa,kamar Saudiya da Masar.

Yan siyasa da dama da kuma masu nazarin alamura da ka je su komo suna ganin cewa wannan rikici zai iya komawa na darika a kasar ta Lebanon data fuskanci yakin basasa har sau biyu.

Gwamnatin Fouad Siniora dai tace babu inda zata,tana mai cewa tattaunawa ce kadai zata kawo karshen halin da ake ciki ba wai zanga zanga ba.

Masu zanga zangar,wadanda suka hada da bangarorin jamiyun kirista sun kakkafa tantuna dauke da hotunan shugaban Hezbolla Hassan Nasrallah da wasu shugabanin adawa,a wani wuri da firaministan kasar yake zaune dare da rana tun lokacinda aka fara zanga zanga,suna masu baiyana cewa ba zasu tashi daga yankin ba har sai sunga abinda ya turewa buzu nadi.

A halin da ake ciki dai ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeire ya isa kasar Syria a yau litinin inda zai bukaci shugaba Bashar al Assad ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

yan adawa da suka hada da wasu kiristoci suna bukatar samun karin iko cikin gwamnati,wadda da hada da ya siyasa na sunni masu kin jinin Syria da kiristoci,da yan Druze.

Sai dai wadannan yan siyasa sunce yan adawa suna neman rage karfin gwamnati ne tare kuma da shashantar da batun kotun MDD da zata tsugunad da wadanda ake zargi da kisan tsohon firaminista Rafik Hariri.