1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rufe Taron SADC

August 17, 2007
https://p.dw.com/p/Btui
Robbert Mugabe na Zimbabwe
Robbert Mugabe na ZimbabweHoto: AP

Shugabannin kasashen kudancin afrika sun kaddamar da rundunar soji na taimakawa tabbatar da zaman lafiya ,a bangaren tsarin nahiyar Afrika na samarda dakarun da zasu kasance cikin shirin kota kwana,domin taimakawa zaman lafiya da shawo kan rigingimu idan suka barkea a nahiyar.

Shugaba Levy Mwanawasa na kasar Zimbia kuma mai masaukin baki,shine ya kaddamar da ayarin rundunar ,inda a gaban sauran shugannin kasashen kudancin Afrika 14 dake halartan taron yankin,ya zaga domin ganewa idanunsa sojojin da a ka jera a karkashin wannan sabon shiri, a birnin Lusaka.

An kaddamar da wannan shiri ne da harbin bindigogi a iska da karan jiragen yaki wadanda ke shawagi a sararin samaniyan birnin.

Mwanawasa dake zama shugaban kungiyar shugabannin yankin kudancin Afrikan na yanzu ,yace dakarun yankin da zaa kira SADC Brigade,zasu taimakawa tsarin samarda zaman lafiya da suka hadarda kwance damarar yaki a yankuna da ake fama da rikici,tarae da bawa alumma dake bukata tallafi,domin rage wahalhalu da suke fama dasu ,da kuma tallafawa a lokacin da aka fuskanci balai daga indallahi.

Rundunar kiyaye zaman lafiyan ,baya ga kokarin nahiyar Afrika na samarda ayarin dakarun soji da zasu kasance cikin shirin kota kwana,nan da shekarata 2010,ana kuma saran zaa iya tura su yankunan bukatu na takaitattccen lokaci,a karkashin inuwar mdd da kungiyar gamayyar Afrika ko kuma kungiyar ta kasashen dake yankin kudancin Afrikan.

Brigadier General Malakia Nakanduungileh,dake kasancewa babban hafsan sashin tsare tsare na rundunar mai barin gado,ya bayyana wannan sabon ayari da kasancewa babbar nasara a bangaren wannan yanki na kudancin Afrika,inda yace a shirye rundunar take ta sauke kowane aiki aka dora mata.

Shugabannin kasashe 14 dake halartan taron na yini biyu da aka bude a jiya a birnin Lusana,kasar Zambia dai sun kuma tabka mahawara dangane dangane da muhimmancin hadin kai da magana da murya guda,da kuma halin da ake ciki a kasar da Zimababwe.

Shugaba Thabo Mbeki dake shiga tsakanin a rikicin siyasar kasar ta Zimbabwe,yace an samu cigaba,ayayinda sauran shugabannin basu nuna alamun tursasawa Shugaba Robbert Mugabe ya yi sauyi a harkokin siyasar kasarsa ba.

Kakakin Mugabae George Charamba yace hakki ya rataya a wuyan sauran kasashen yankin na taimakawa Zimbabwe rage matsalolinta kuma bazasu wuce wannan iyaka ba.

Shugaba Mwanawasa na Zanbia dai shine shugaban Afrika na farko daya fito fili wajen shawartan Mugabe da yayi kokarin gyara harkokin gudanarwa wannan kasa,alokacin ziyarar daya kai a Namibia a wannan shekara.